Yan Sanda Sun Yi Babban Kamu, Wanda Ake Zargi da Kashe Surukin Gwamna Ya Shiga Hannu

Yan Sanda Sun Yi Babban Kamu, Wanda Ake Zargi da Kashe Surukin Gwamna Ya Shiga Hannu

  • Ƴan sanda sun kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da kisan surukin gwamnan Bayelsa, basarake da wani shugaban al'umma
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar Bayelsa ya ce sun samu waya a hannun wanda ake zargin, kuma tuni ya fara ba da haɗin kai wajen bincike
  • Jami'in ya ce sun samu sautin murya a wayar wanda aka kama, inda suka ji waɗanda ake zargi da kisan na jero masu ɗaukar nauyinsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bayelsa - Rundunar ‘yan sanda a jihar Bayelsa ta kama daya daga cikin wadanda ake zargi da kashe Odeinyefa Ogbolosingha, surukin Gwamna Douye Diri.

Ana zargin sun kashe surukin gwamna, sarkin kauyen Kalaba, Kolibo Amabelimo, da shugaban ƙungiyar al'umma (CDC), Samuel Oburo, a yankin Kalaba da ke karamar hukumar Yenagoa.

Yan sanda.
Yan sanda sun kama wadanda suka kashe surukin gwamna a Bayelsa Hoto: @PoliceNG
Source: Getty Images

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Francis Idu, shi ne ya tabbatar da hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Yenagoa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Matashi ya kashe mahaifinsa bayan sassara wuyansa da adda a Jigawa

Waɗanda ake zargi da kisan surukin gwamna

Francis Idu ya ce ce ana zargin mutane uku da hannu a kisan, waɗanda suka haɗa da Gideon Atama (32), Bethlehem Nwanlia (49), da Clever Ovo (33).

Kwamishinan ya bayyana cewa daya daga cikin wadanda ake zargi, Bethlehem Nwanlia, ya rasu, yayin da sauran kuma suka gudu har yanzu ba su shiga hannu ba.

Sai dai a cewarsa, Clever Ovo, wanda ke tsare a hannun ‘yan sanda, ya amsa cewa su ‘yan kungiyar ta’addanci ce da ake kira Endurance Amagbein.

Kwamishinan ya ce shugaban wannan gungun, wanda sojoji ke nema ruwa a jallo, na da hannu a kisan sojoji 16 da aka yi a Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Arewa, jihar Delta.

Ƴan sanda sun fara samun bayanai

Francis Idu ya ce:

“Mun kama Gideon Atama dauke da wayar hannu da kuma kayan sojoji. Daga cikin wayar mun gano hotunan bindigogi da kuma sautin murya na laifukan da suke yi.

Kara karanta wannan

Turji ya zafafa hare-hare a Sakkwato, mazauna kauyuka 20 sun fara kaura

"Sannan kuma a sautin muryar, sun faɗi wasu da suke daukar nauyinsu wajen lalata kayayyakin gwamnati a yankin.”

An kama dattijo da hannu a fasa bututun mai

A wani ci gaban, ‘yan sanda da ke aiki da rundunar tsaron ruwa a Igbikiba, karamar hukumar Southern Ijaw, sun kama wani dattijo, Daniel Williams, da ake zargi da hannu a lalata bututun man fetur.

Ana zargin Daniel da hannu a harin da aka kai kan bututun Tebedaba-Brass da ke Lakosogbene a karamar hukumar Southern Ijaw, Punch ta ruwaito.

Rundunar ‘yan sanda ta ce bincike ya yi nisa, kuma za a ci gaba da kama sauran wadanda ke da hannu a irin wadannan laifuka.

Ƴan sanda sun gwabza da jami'an Amotekun

A wani labarin, kun ji cewa faɗa ya kaure tsakanin dakarun ƴan sanda da jami'an Amotekun kan wani mutumi da aka kama bisa zargin sata a jihar Ondo.

Rahotanni sun bayana cewa jami'an Amotekun sun yi harbe-harbe, lamarin da ya tada hankulan jama'a a birnin Akure.

Rigimar ta ƙara tsananta ne a kusa da filin ShopRite da ke daf da hedikwatar Amotekun, da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262