An Sake Sako Dangote a Gaba domin Durkusa Matatar fetur da Ya Yi a Legas
- Shugaban kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa har yanzu yana fuskantar barazana a matatarsa da ya kashe $20bn wajen ginawa
- Aliko Dangote ya zargi wasu mutane da suka dade suna cin gajiyar shigo da fetur da tallafi, da yunkurin ganin matatar ba ta yi nasara ba
- Dangote ya bayyana cewa duk da haka, yana da tabbacin zai yi nasara a kan wadanda ke kokarin hana cigaba da aikin matatar dake Lekki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Aliko Dangote ya sake bayyana cewa akwai wasu mutane da ke ci gaba da kawo cikas ga ci gaban matatar man fetur dinsa da ke Lekki, jihar Legas.
Hakan na zuwa ne bayan dan kasuwar ya yi korafi kan matatar a kwanakin baya bayan kaddamar da ita.

Source: Getty Images
Dangote ya bayyana haka ne yayin wani taron masu zuba jari da aka gudanar a Legas, kamar yadda jaridar Semafor ta ruwaito.
Dangote, wanda shi ne attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika, ya ce ya shafe shekaru yana fafutukar ganin wannan aiki na Dala biliyan 20 ya kammala, duk da cikas daga wasu manya.
Dangote na fuskantar kalubale kan matatar mai
Dangote ya ce wasu mutane da suka shafe dogon lokaci suna samun riba daga tallafin fetur da gwamnatin Najeriya ke bayarwa, na daga cikin wadanda ke kokarin dakile aikin matatar.
Punch ta wallafa cewa Dangote ya ce:
“Wadanda suka fi cin gajiyar shigo da fetur da tallafi ne ke daukar nauyin adawa da cire tallafin fetur da gwamnatin Tinubu ta yi,
"Kuma su ke kokarin hana matatarmu yin aiki yadda ya kamata.”
Ya ce kungiyoyi da kamfanonin na amfani da kudi da tasirinsu wajen hana matatar ta samu isasshen danyen mai gami da goyon baya daga hukumomin gwamnati.
"Zan yi nasara a karshe" — Dangote
Duk da haka, Dangote ya nuna kwarin guiwa cewa zai samu nasara a kan kalubalen da ke gaban sa, inda ya bayyana kansa a matsayin wanda ya saba da fafutuka a rayuwar shi.
Aliko Dangote ya ce:
“Har yanzu muna fafutuka kuma rikicin bai kare ba. Amma na saba da gwagwarmaya tun da dadewa, kuma ina da tabbacin zan ci nasara a karshe,”
A baya, Dangote ya zargi wasu manyan kamfanonin man fetur na duniya da hana matatar tasa isasshen danyen mai, duk da yarjejeniyar da ke tilasta su sayar da danyen mai ga matatar.

Source: UGC
Dangote ya ce duk da irin wadannan matsaloli, zai tabbatar da cewa matatar ta yi aiki yadda ya kamata, yana mai cewa zai ci gaba da jajircewa har sai ya cimma burinsa.
Dangote ya samu matsayi a bankin duniya
A wani rahoton, kun ji cewa wanda ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote ya samu matsayi a bankin duniya.

Kara karanta wannan
Ba EFCC ke tsare da ni ba: Mele Kyari ya karyata jita-jitar EFCC ta yi masa kamun kazar kuku
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya taya dan kasuwar murnar samun matsayin da ya yi a fadin duniya.
Bola Tinubu ya ce yana da tabbas Aliko Dangote zai yi aiki da matsayin da ya samu wajen kawo cigaba Najeriya da duniya baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

