An Gano Illar Rikicin Filaye a Najeriya bayan An Salwantar da Rayuka kusan 2000

An Gano Illar Rikicin Filaye a Najeriya bayan An Salwantar da Rayuka kusan 2000

  • An bankado yadda rikici a kan filaye da iyakokin kasa ke haddasa asarar rayuka da dama a sassan Najeriya daban-daban
  • Bincike da wata kungiya ta PIND ta wallafa ya nuna yadda aka salwantar da rayuka akalla 1,796 daga watan 2018 zuwa 2025
  • Rahoton ya nuna yankunan Kudu da Arewa ta Tsakiya sun fi fuskantar tasirin wannan tashin hankali a kan matsalar fili

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kimanin mutane 1,796 sun rasa rayukansu a rikice-rikicen iyaka da na al’umma a Najeriya tsakanin Janairu 2018 da Agusta 2024.

An samo wannan adadi ne daga rahotannin kafofin yada labarai da binciken da Kungiyar Goyon Bayan Hadin Kan Al’umma a Delta ta gudanar.

Tinubu
Rayuka akalla 2000 sun salwanta a Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Punch News ta wallafa cewa rahoton ya bayyana cewa a tsakanin 2018 zuwa 2022 kadai, an kashe mutane 676 a rikice-rikicen irin wannan.

Kara karanta wannan

Turji ya zafafa hare-hare a Sakkwato, mazauna kauyuka 20 sun fara kaura

Rikicin filaye: An samu karuwar kashe-kashe

Adadin ya tashi sosai a cikin shekarun da suka biyo baya, wanda ke nuna karuwar tsanani da yawan rikice-rikicen al’umma, musamman a kudu da kuma Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Rahoton PIND ya kara da cewa a jihar Cross River kadai, an samu fiye da mutanen 400 da suka rasa rayukansu tsakanin Janairu 2020 da Disamba 2023.

“Rikice-rikicen al’umma, musamman wadanda suka shafi jami’an tsaro na gwamnati, sune manyan sanadin tashin hankali a Delta da Bayelsa, Rikice-rikicen al’umma sun haifar da asarar rayuka fiye da 650 a jihohin guda biyu tsakanin Janairu 2020 zuwa Disamba 2023.”

Rikice-rikicen suna da nasaba da takaddamar ƙasa da kuma rashin fahimtar juna tsakanin al’umma a kan iyakokin filayensu.

Shugaba
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kungiyar ta ce rikice-rikicen a Okuama a Delta da Igbomotoru a Bayelsa da ke jawo asarar rayuka, saboda takaddamar ƙasa da kuma rikicin tsaro, abu ne da za a iya kawo karshensu.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da neman hatsabibin ɗan bindiga Bello Turji, yaransa sun yi ta'asa a Sokoto

An kashe bayin Allah wajen rikici a Kogi

A wani rikici mai munin gaske da aka samu a Agbudu na Kogi a watan Yuli 2020, an kashe mutane 14, an ruwaito cewa 13 daga cikin su 'yan gida daya ne.

A watan Yuni 2023, rikici na ƙasa a Oju, Binuwai, ya yi sanadin rasuwar mutane 14, yayin da a watan Agusta 2023, mutane hudu sun mutu a rikicin mallakar ƙasa tsakanin al'ummomin Oyofo da Awha a Enugu.

A watan Fabrairu 2023, an kashe mutane shida a rikici tsakanin al'ummomin Omor da Anaku a Anambra.

A watan Afrilu 2025, wani rikici ya faru a Ebonyi, ya yi sanadin kashe mutane shida, ciki har da mace mai juna biyu, a rikici tsakanin al'ummomin Ndukwe da Okporojo.

Kashe-kashe ya sa an fara barin Sakkwato

A baya, mun wallafa cewa hare-hare da ake zargin 'yan bindigan da ke tare da Bello Turji ne suka kai, sun haddasa mummunan yanayi ga al’ummar wasu yankuna na jihar Sakkwato.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta dare gida 2, an samu hatsaniya kan Seyi Tinubu

Munanan hare-haren sun fara tilastawa mazauna kauyuka akalla 20 barin gidajensu, yayin da suka tafi cikin gari domin tsira da harin da za a iya kawo wa a nan gaba kadan.

Wasu daga cikin kauyukan da aka tabbatar da cewa jama’arsu sun tsere sun haɗa da Makira, Shabanza, Katsalle, Dan Kura, Garin Tunkiya, Dama, Dan Tazako I, II da III, da Gaugai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng