An Kama Wanda aka Dauka Haya domin Kashe Kashe a Filato da Bindiga
- Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta kama wani matashi mai suna Joseph Babari da ake zargi da safarar makami da harsasai ba bisa ka’ida ba
- Wanda ake zargin na dauke da bindiga kirar gida da harsasai takwas da kayan tsafi lokacin da aka cafke shi a wani binciken tsaro a hanyar Gombe
- Rundunar ta ce binciken farko da ta gudanar ya nuna an dauki matashin haya ne domin yin fada a wani yanki da rikici ke faruwa a jihar Filato
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - A kokarin dakile yaduwar makamai ba bisa ka’ida ba, rundunar ‘yan sanda a Gombe ta kama wani mutum dauke da makami a iyakar jihar da Taraba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan sanda sun kama wanda ake zargin ne a ranar 30 ga Afrilu da daddare.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya wallafa a Facebook a ranar Asabar 3 ga Mayu 2025.
An bayyana cewa wanda ake zargin ya fito ne daga Maikatako a karamar hukumar Bokos ta jihar Filato, inda ya ce yana kan hanyarsa zuwa Karim Lamido a jihar Taraba.
An kama wanda ya fito daga Filato da bindiga
Rundunar ta ce tawagar ‘yan sanda a yankin Pero-Chonge a karamar hukumar Shongom ne ta kama Joseph Babari mai shekara 27.
An ruwaito cewa Joseph Babari dan asalin yankin Bambur Darufa ne a jihar Taraba kuma an kama shi ne da misalin karfe 11:30 na dare.
Kayan da aka kama da shi sun hada da bindiga kirar gida, harsasai takwas, rigar yaki da kuma kunshin kayan tsafi a jikinsa.

Source: Facebook
Lokacin da aka fara tambayarsa, Joseph ya amsa cewa yana tafiya ne daga jihar Plateau zuwa Taraba.
Amma daga baya bincike ya gano cewa an dauke shi aiki ne domin yin fada a Bokos a kan N180,000 na wata biyu.
'Yan sanda za su cigaba da bincike
Rundunar ‘yan sanda ta ce wanda ake zargin yana tsare a hannunsu tare da kayan da aka kama shi da su.
Baya ga haka, rundunar ta tabbatar da cewa bincike na ci gaba domin gano daga ina makamin ya fito da kuma wanda ya dauke shi aiki.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Bello Yahaya, ya jaddada kudurin rundunar wajen hana yaduwar makamai da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ya bukaci jama’a su rika ba da bayanai cikin gaggawa kan duk wani motsi da ba su yarda da shi ba domin taimakawa jami’an tsaro.
An kashe limamin Juma'a a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kashe limamin Maru a jihar Zamfara.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe Alkali Salihu Sulaiman ne bayan an sace shi a watan Ramadan.
Bayan kisan gillar da aka yi wa limamin, 'yan bindigar sun kashe uku daga cikin iyalan shi duk da kudin fansa da suka karba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

