Ana tsaka da Neman Hatsabibin Ɗan Bindiga Bello Turji, Yaransa Sun Yi Ta'asa a Sokoto

Ana tsaka da Neman Hatsabibin Ɗan Bindiga Bello Turji, Yaransa Sun Yi Ta'asa a Sokoto

  • Ƴan bindiga da ake zargin yaran Bello Turji ne sun kai farmaki garuruwan Satiru, Makwaruwa da Gidan Gyara a Isa dake jihar Sokoto
  • Al’ummomin da aka kai harin sun shiga tsoro da rudani, yayin da mutane suka fara tserewa daga gidajensu domin neman mafaka
  • Wannan farmakin na cikin jerin hare-haren da ake kaiwa a yankin, inda ake fama da matsanancin rashin tsaro da yawaitar sace-sace
  • Rahotanni sun ce babu wanda aka tabbatar da mutuwarsa a halin yanzu, amma jama'a na cikin fargaba da tsananin tashin hankali

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu daga cikin yaran hatsabibin ɗan bindiga, Bello Turji sun kai hari a jihar Sokoto.

A daren jiya Juma'a 2 ga watan Mayun 2025, yaran Bello Turji sun kai farmaki a Satiru, Makwaruwa da Gidan Gyara.

Kara karanta wannan

Bayan shafe makonni 2 a kasar Jamus, gwamnan da Tinubu ya dakatar ya dawo Rivers

Yaran Bello Turji sun sake kai farmaki a Sokoto
Yayin da sojoji ke neman Bello Turji ruwa a jallo, yaransa sun kai hari a Sokoto. Hoto: Legit.
Source: Original

Majiyar Bakatsine da ke kawo rahoto kan matsalolin tsaro ita ta tabbatar da haka a daren jiya Juma'a a shafin X.

Bello Turji ya sauya salon yaƙi a Arewa

Hakan bai rasa nasaba da rahoton Legit Hausa da ta kawo kwanakin baya cewa Bello Turji ya sauya salon yaki da sojoji.

Rahotanni sun nuna 'yan bindiga fiye da 200 sun tsere daga dazukan Zamfara zuwa yankin Isa da Sabon Birni a jihar Sokoto.

An ce hare-haren sojoji a Danjibga da wasu dazukan Kudancin Zamfara ne suka tilasta wa 'yan bindigar guduwa daga maboyarsu.

Rahoton ya nuna 'yan bindigar na amfani da dazukan Gusami, Rugu da Rukudawa suna shiga Dutsi har zuwa Fakai da yankin Isa.

Ana zargin shahararren 'dan bindiga, Bello Turji, yana da hannu wajen shirya wannan sauya matsugunin tare da jagorantar komai.

Yaran Bello Turji sun kai wani hari a Sokoto
An ruwaito cewa yaran Bello Turji sun farmaki ƙauyuka a Sokoto yayin da sojoji ke nemansa. Hoto: @ahmedaliyusok.
Source: Twitter

Yaran Turji sun jefa al'umma cikin fargaba

Kara karanta wannan

Ranar ma'aikata: Sababbin bukatun da kungiyoyin kwadago suka tura ga Tinubu

Rahotanni suka ce lamarin ya faru ne a cikin karamar hukumar Isa da ke jihar Sokoto a Arewa maso Yammacin Najeriya.

An jefa tsoro da rudani a wadannan garuruwa, inda jama’a suka shiga firgici saboda harin da aka kai musu.

Wata majiya ta ce:

“Babu wanda aka tabbatar da mutuwarsa a yanzu, muna kokarin taimaka wa wadanda abin ya shafa."

Wannan ba shi ne karon farko ba da ake zargin masu biyayya ga Bello Turji ke kai hari a jihohin Sokoto da Zamfara har ma da Katsina.

Wasu na ganin hakan bai rasa nasaba da daukar fansa kan abubuwan da sojoji ke yi musu na kisan ƴan uwansu da aka yi.

Sai dai wasu na ganin matsin lamba da ake yi wa mai gidansu ya sanya su yin haka domin nuna tasirinsa.

Yan bindiga sun kai wani hari a Sokoto

Mun ba ku labarin cewa wasu yan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Sokoto a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Miyagun sun farmaki ƙauyen Illela-Baraya a ƙaramar hukumar Gwadabawa a daren ranar Juma'a, 25 ga watan Afrilun 2025.

Yayin harin da aka kai a ƙauyen, an hallaka mutum uku bayan sun buɗe wuta kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.