Bayan Shafe Makonni 2 a Kasar Jamus, Gwamnan da Tinubu Ya Dakatar Ya dawo Rivers
- Gwamna Siminalayi Fubara ya dawo daga hutun da ya je kasashen waje, inda aka tarbe shi a filin jirgin Omagwa da yammacin Juma'a
- Rahotanni sun nuna cewa Fubara ya gana da Shugaba Tinubu a Landan don lalubo mafita ga rikicin siyasar jihar Rivers mai cike da hatsaniya
- A ziyarar sirri, Fubara ya kai wa Wike ziyara tare da gwamnonin Ogun, inda ya durkusa gaban Wike yana roƙon sulhu da zaman lafiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rivers - Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar da shi, Siminalayi Fubara, ya dawo daga hutu na makonni biyu da ya shafe a kasashen waje, ciki har da Jamus.
An samu labarin cewa Gwamna Fubara ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Omagwa, Fatawal, babban birnin Rivers, da karfe 7:00 na yammacin Juma'a.

Source: Twitter
Gwamna Fubara ya dawo Rivers bayan mako 2
Wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna gwamnan a cikin filin jirgin saman, inda ya samu tarba daga wasu mukarrabansa, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa an yi wa gwamnan rakiya zuwa wata motar zirga-zirga da aka ajiye a filin domin daukarsa, inda ta tashi nan take bayan shigarsa.
A lokacin da ya ke hutun, an ce Fubara ya sanya labule da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Landan, a lokacin da ya je kasar hutun aiki.
Fubara ya gana da Tinubu a Landan
Wani rahoton jaridar Africa Report ya nuna cewa, Tinubu da Fubara sun gana a Landan, da nufin tattauna wa kan yadda za a dawo da zaman lafiya a jihar Rivers.
Wani jami’in gwamnati da yake da masaniya kan taron, ya kara da cewa an shirya taron ne domin shawo kan rikicin siyasar da ya mamaye jihar mai arzikin mai.

Kara karanta wannan
Uwar Bari: Fubara zai kara zama da Wike a shirin sulhu a Rivers, APC da PDP sun magantu
A cewar jami’in:
“Taron ya zama wani yunkuri daga Shugaba Tinubu domin nemo mafita mai dorewa ga rikicin siyasa da ake ci gaba da fuskanta a wannan jiha.”
Hakazalika, an rahoto cewa, a 'yan tsakanin ne Fubara ya kai ziyara ga Nyesom Wike, ministan Abuja kuma tsohon gwamnan Rivers.

Source: Facebook
Fubara ya gana da Wike a gidansa
Premium Times ta ji daga majiyoyi cewa gwamnan Ogun, Dapo Abiodun da kuma Olusegun Osoba, tsohon gwamnan Ogun ne suka yi wa Fubara jagoranci zuwa gidan Wike.
Wata majiya, ta shaida cewa:
“An kawo Fubara gidan minista a ranar Jumma’a, 18 ga Afrilu. Ya durkusa har gwiwa gaban Wike, ya rike da kafafunsa yana kiran shi da 'Oga na’."
Majiyar ta ce Fubara ya zauna a gidan wike har zuwa safiyar Asabar, 19 ga Afrilu, kuma ana sa ran tattaunawar tasu ta haifar da da mai ido.
Duk da cewa babu bayani kan taron a hukumance, amma an ji cewa an umurci Fubara da ya tattara magoya bayansa a Rivers, musamman dattawan garin, sannan ya bayyana musu “gaskiyar” kan dalilin rikicinsa da Wike.
Fubara zai sake ganawa da Wike
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ana sa ran za a sake wani zama tsakanin Siminalayi Fubara da Nyesom Wike domin kammala shirin sulhu, don dawo da zaman lafiya a Rivers.
Tun bayan kammala zaben 2023 ne aka fara samun sabani tsakanin Wike da Fubara, wanda hakan ya janyo rikicin siyasa a Rivers, da ya sa aka ayyana dokar ta baci a jihar.
Sai dai, an ce gwamnan Ogun, Dapo Abiodun da kuma Olusegun Osoba, tsohon gwamnan Ogun, na kokarin ganin Fubara da Wike sun daidaita kansu domin samun maslaha.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

