Shugaba Tinubu Ya Samo Mafita ga Gwamnonin Najeriya kan Masu Sukarsu

Shugaba Tinubu Ya Samo Mafita ga Gwamnonin Najeriya kan Masu Sukarsu

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba gwamnonin Najeriya shawara kan masu sukar ayyukan da suke gudanarwa
  • Mai girma Bola Tinubu ya buƙaci gwamnonin da su yi watsi da masu sukarsu tare da maida hankali kan ayyukan da suke gudanarwa
  • Shugaban ƙasan ya kuma shawarci gwamnonin da su sanya al'umma a cikin shirye-shiryen da suke ƙoƙarin aiwatarwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnonin Najeriya da su yi kunnen uwar shegu da masu sukar aikinsu.

Shugaba Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohi 36 na Najeriya da su mayar da hankali wajen kawo sauye-sauye na ainihi da za su inganta rayuwar al’umma kai tsaye.

Tinubu ya ba gwamnoni shawara
Shugaba Tinubu ya bukaci gwamnoni su yi watsi da masu sukarsu Hoto: @DOlusegun, @NGForum
Source: Facebook

Bola Tinubu ya kai ziyara jihar Katsina

Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya fara a jihar Katsina, cewar rahoton jaridar The Cable.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Rarara ya cashe da sabuwar waƙa a liyafar da aka shiryawa Tinubu a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin ziyarar, shugaban ƙasan ya ƙaddamar da muhimman ayyukan ci gaba da Gwamna Dikko Radda na jihar ya kammala.

Daga cikin ayyukan da ya ƙaddamar har da hanyar Eastern Bypass mai tsawon kilomita 24 wacce ta haɗe hanyar Dutsin-ma da Yandaki a ƙaramar hukumar Kaita, ta hanyar Kano da Daura.

Wace shawara Tinubu ya ba gwamnoni?

Mai girma Bola Tinubu ya buƙaci gwamnonin da su yi watsi da masu sukarsu, waɗanda ke ƙoƙarin karkatar musu da hankali daga yin ayyukan raya ƙasa.

“Ku sanya al’umma a tsakiyar shirye-shiryenku. Ayyukanku na gaskiya da jajircewarku za su amsa kowace irin suka. Ka da ku damu da hayaniya, sakamakon aikinku shi ne zai yi magana da kansa.”
“Mun yanke shawarar maida hankali kan zaman lafiya da kwanciyar hankali."
“Na san kuna fama da ta'addanci hare-haren ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane a jihar nan, amma kun nuna ƙwazo da jarumta wajen ganin Katsina ta ci gaba."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Okowa ya bayyana lokacin da Atiku zai fice daga jam'iyyar PDP

"Ba za mu ƙyale ku haka ku kaɗai ba. Gwamnatin tarayya za ta kasance tare da ku.”

- Bola Ahmed Tinubu

Tinubu ya gano matsalolin Najeriya

Shugaban ƙasan ya bayyana yunwa da talauci a matsayin manyan barazana ga zaman lafiya a Najeriya.

Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya ce yunwa barazana ce ga kasar nan Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter
"Tattalin arziƙin ƙasa yana tafiya a hanyar da ta dace. A yau muna ganin ƙoƙari na kawar da yunwa da ƙudirin samar da isasshen abinci da ƙarfafa al’umma."
“Za a ƙarfafa noma na ci da na sayarwa. Da zarar mun kuɓuta daga yunwa, za mu ƙara jin dadin zaman lafiya da hafin kai."

- Bola Ahmed Tinubu

Tinubu ya gargaɗi masu son tarwatsa Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ja kunnen mutanen da ke son tarwatsa Najeriya.

Shugaban ƙasan ya bayyana cewa Najeriya ba za ta saduda ba a ƙoƙarin da take yi na yaƙar masu ƙoƙarin ganin bayanta.

Mai girma Bola Tinubu wanda ya bayyana hakan ga sojoji a Katsina, ya kuma yaba da irin jajircewa da sadaukarwar da suke yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng