Al'umma Sun Samu Sauƙi bayan Kisan Fitinannen Ɗan Bindiga da Ya Addabi Arewa
- Jami'an tsaro sun kashe Aungwa Sesugh, wanda aka fi sani da Tino Brown, a harin safiyar yau Alhamis a Zaki-Biam da ke jihar Benue
- An kama Sesugh da bindigar gargajiya da harsasai uku da kuma kayan sihiri, bayan samun bayanan sirri daga wata kungiyar Akumave da ta ɓalle
- Bayan an kama shi, ya amsa cewa yana cikin masu garkuwa da shugaban karamar hukumar Ukum, kuma ya kai 'yan sanda zuwa inda makamai suke
- Yayin da suka isa garin Tse-Shor, 'yan bindigan sun bude wuta, harbin da aka yi ya kashe Sesugh, sauran kuma suka tsere cikin daji
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Jami'an tsaro sun yi nasarar aika kasurgumin dan bindiga lahira da ya addabi al'ummar jihar Benue.
Hatsabibin ɗan bindiga, Aungwa Sesugh, wanda aka fi sani da Tino Brown ya mutu yayin musayar wuta da sojoji.

Source: Original
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da labarin a yau Alhamis 1 ga watan Mayun 2025 a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yan bindiga suka ce basarake a Benue
Wannan nasara na jami'an tsaro na zuwa ne bayan sanar da sace wani basarake a jihar Benue da ke fama da matsalolin rashin tsaro.
Wasu ’yan bindiga sun sace dagacin kauyen Dickson Idu a farmaki da suka kai da yamma a karamar hukumar Ohimini ta jihar Benue.
Dakarun soji da ’yan sanda da jami’an tsaron farar hula sun fara bincike da sintiri don gano inda aka boye dagacin a cikin daji.
A wani farmaki na daban, rundunar ’yan sanda ta hallaka wani babban dan bindiga da ya addabi yankin Zaki-Biam na jihar.

Source: Facebook
Yadda aka hallaka fitinannen ɗan bindiga a Benue
Majiyoyi suka ce shahararren dan bindigan ya mutu a musayar wuta da jami'an tsaro a Zaki-Biam a jihar Benue da ke tsakiya Najeriya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an cafke Sesugh da bindiga da kayan sihiri da misalin karfe 1:30 na asuba.
Bayan tambayoyi, Sesugh ya amsa cewa yana da hannu a laifuka da dama, ciki har da sace shugaban karamar hukumar Ukum Nulge.
An ce ɗan ta'addan ya kai 'yan sanda zuwa kauyen Tse-Shor, amma 'yan uwansa suka bude wuta domin kokarin kwato shi.
Harbin da ya same shi ne ya yi sanadin mutuwarsa a asibiti yayin da sauran miyagun sun tsere da kafafunsu
Tsaro: Gwamnan Benue ya nemi taimakon Tinubu
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana cewa abin da al’ummarsa ke buƙata yanzu shi ne cikakken goyon bayan gwamnatin tarayya, ba dokar ta-baci ba.
Gwamna Alia ya ce matsalar tsaro da ake fuskanta a jihar ba ta fi ƙarfinsa ba, amma yana neman taimako sosai domin ya kori makiyaya masu ɗauke da makamai a fadin jihar.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ta rage yawan kananan hukumomin da ake kai hare-hare daga 17 zuwa shida bayan hawansa kan mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

