Bankunan Najeriya za Su Fara Cire N6 kan Kowane Saƙon da Suka Tura
- Daga yau Alhamis, 1 ga Mayu, 2025, bankuna a Najeriya za su fara cire N6 kan kowanne saƙon da suke turo wa abokan huldarsu
- Karin farashi ya biyo bayan ƙarin kudin da kamfanonin sadarwa suka yi kan saƙonni bisa amincewar gwamnatin tarayya
- Bankuna sun bayyana cewa za a ci gaba da biyan kuɗin ne har sai dai idan abokin hulda ya canza tsarin karɓar saƙon kar-ta-kwana
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bankunan Najeriya sun sanar da sabon tsarin cire N6 daga asusun abokan hulɗarsu kan kowanne saƙon da aka turo ta wayar salula.
Wannan karin ya fara aiki ne daga yau Alhamis, 1 ga watan Mayu, 2025, kamar yadda bankunan suka sanar cikin saƙon da suka aikewa abokan huldarsu da safiyar Laraba.

Source: Getty Images
Jaridar Vanguad ta wallafa cewa wasu bankunan sun ba da damar fita daga tsarin karbar sakonni domin kaucewa cire kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da farko, ana cire N4 ne kan kowanne saƙon bayanin ma’amala, amma yanzu an ƙara N2 saboda ƙarin farashin da kamfanonin sadarwa suka yi, bisa yardar gwamnatin tarayya.
Dalilin karin kudin SMS da bankuna suka yi
A cikin saƙon da ɗaya daga cikin bankunan Najeriya ya tura wa abokan cinikinsa, an bayyana cewa:
“Ya abokin hulda, don Allah a lura cewa daga ranar Alhamis, 1 ga Mayu 2025, za a ƙara kuɗin da ake cirewa kan saƙon alat daga N4 zuwa N6.
"Sauya tsarin ya biyo bayan karin da kamfanonin sadarwa suka yi.”
Baya ga haka, bankunan sun kuma jaddada muhimmancin saƙonnin turawa da shigar kudi ga abokan huldarsu.
Daily Trust ta wallafa cewa bankunan sun bayyana cewa saƙonnin na taimakawa kwastomomi su rika lura da duk wata mu’amalar kudi da ke faruwa a asusunsu.
Za a fi cajin lambobin ƙasashen waje
Bankunan sun kuma bayyana cewa idan za a tura sako su zuwa lambobin da ke waje — wato na ƙasashen waje — to za a ƙara caji mai yawa a kan irin waɗannan lambobin.
Haka kuma, an baiwa kwastomomi damar canza hanyar samun sakon daga SMS zuwa imel ko ta manhajar bankin idan ba su son biyan karin kuɗin.

Source: Getty Images
Wannan sabon karin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya da dama ke koka kan hauhawar farashin kayayyaki da sabis daban-daban a ƙasar.
Ana sa ran cewa karin kuɗin SMS ɗin zai haifar da ƙarin matsin lamba ga al’ummar da ke fuskantar matsalolin tattalin arziki.
CBN ya karyata kawo sababbin takardun kudi
A wani rahoton, kun ji cewa babban bankin Najeriya na CBN ya karyata cewa ya kirkiro sababbin takardun kudi da za a rika aiki da su.
Bankin ya bayyana haka ne bayan yawaitar jita jita tare da nuna wasu hotunan takardun kudi ana cewa za a fara aiki da su a Najeriya.
CBN ya yi kira ga 'yan Najeriya da zu daina yarda da duk wani labari da suka gani a shafukan sadarwa marasa inganci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

