ACF: Dattawan Arewa Sun Gindaya Sharadin Goyon Bayan 'Dan Takara a Zaben 2027

ACF: Dattawan Arewa Sun Gindaya Sharadin Goyon Bayan 'Dan Takara a Zaben 2027

  • ACF ta ce Arewa za ta mara wa 'yan takarar 2027 baya ne kawai idan suna da gaskiya, rikon amana da kishin muradun yankin
  • Kungiyar ta nuna damuwa kan matsalolin tattalin arziki, tsaro da rashin shugabanci nagari da ke addabar Arewa a halin yanzu
  • Dattawan Arewa suna soki fara kamfen tun da wuri, su na cewa hakan na dauke hankalin gwamnati daga amatsalolin talakawansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaKungiyar ACF ta bayyana cewa Arewa za ta mara wa 'yan takarar da za su tsaya a zaben 2027 baya ne kawai idan suka kuduri aniyar kare da inganta muradun yankin.

Alhaji Bashir Dalhatu, shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin bude taron kwamitin a Kaduna.

Kara karanta wannan

El-Rufa'i ya gano wanda ya fi dacewa ya mulki Najeriya a 2027

Arewa
Alhaji Bashir Dalhatu ya ce mai kishin Arewa kawai za su mara wa baya Hoto: Muhammad Lawan
Source: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an shirya taron ne domin tattauna muhimman matsalolin da ke addabar yankin Arewa da kasa baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsayar ACF a kan dan takara a zaben 2027

Alhaji Dalhatu, tsohon Ministan Wuta da Karafa, ya jaddada Arewa ba za ta takaita goyon bayanta ga wani dan siyasa ko jam’iyya ba, inda ya ce nagartar mutum kawai za a duba.

A cewarsa:

“Arewa ba za ta jajirce ga wani dan siyasa ko jam’iyya ba, sai dai ga wadanda ke damuwa da sha’anin yankinmu kuma masu son kare da bunkasa muradunmu.”

Ya kara da cewa Arewa na bibiyar yadda jami’an gwamnati ke gudanar da aikinsu, musamman a matakin tarayya.

Arewa
Wasu daga ckin shugabannin Arewa Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Ya kara da cewa akwai yiyuwar su kafa wani kwamiti da zai tantance shirye-shiryen gwamnati da manufofinta.

'Yan ACF sun koka a kan matsalolin Arewa

Tsohon Ministan ya bayyana cewa yankin Arewa na fama da dimbin kalubale, don haka sai wanda ke da hangen nesa ne kadai zai dace da samun goyon bayan yankin.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An bukaci Tinubu ya ajiye Shettima, ya dauki Kiristan Arewa a 2027

Ya ce:

“Arewa na fama da matsaloli masu yawa da ke barazana ga rayuwarta. Amma abin da babu shakka a kai shi ne Arewa na da dimbin albarkatu da zai ba ta damar yin gogayya da kowane yanki a Najeriya, har ma da nahiyar Afrika baki daya.

Kungiyar ACF ta yi magana kan kamfe tun yanzu

Kungiyar ACF ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda ake fara kamfen tun kafin lokaci gabanin zaben 2027, tana gargadin cewa wannan zai jawo matsala ga mulki.

A cikin wadanda suka halarci taron akwai tsofaffin gwamnoni hudu: Ibrahim Shekarau (Kano), Ramalan Yero (Kaduna), Simon Lalong (Filato), da Ahmed Makarfi (Kaduna).

Sai tsohon Ministan yada labarai, Lai Mohammed; tsohon kakakin rundunar soji, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman (rtd); tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal; da tsohon hadim Kashom Shettima, Dr Hakeem Baba-Ahmed da sauransu.

ACF ta soki kalaman Sakataren gwamnati

A baya, kun ji cewa Kungiyar Arewa ta ACF ta soki sakataren gwamnati kan kalaman da ke cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2031.

Kara karanta wannan

Sola a Aso Villa: Gwamnati ta fadi biliyoyin da take kashewa a biyan kudin wuta

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya bayyana cewa kamata ya yi a mayar da hankali ne kan yadda za a farfado da rayuwar al’umma.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sauke nauyin da ke wuyanta ta hanyar bijiro da hanyoyin da za su inganta rayuwar talakawan Najeriya, musamman a tsaro da tattalin arziki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng