Canza Naira: Kotu Ta Yanke Hukunci a kan Tuhumar da ake Yiwa Buhari da Emefiele
- Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi fatali da karar da wani lauya, Uthman Isa Tochukwu, ya shigar yana tuhumar sauya fasalin Naira
- Tochukwu ya shaida wa kotu cewa tsarin ya tauye masa ‘yancin walwala da mutuncin ɗan adam saboda karancin takardun kudi a lokacin
- Lauyan ya nemi kotu ta tilasta wa Muhammadu Buhari da tsohon shugaban CBN, Godwin Emefiele biyan sa Naira biliyan ɗaya a matsayin diyya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da wani lauya ya shigar kan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Lauyan ya maka tsohon shugaban kasa da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele a gaban kotu ne a kan batun sauya fasalin takardun kudin Naira.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa lauya mai suna Mista Uthman Isa Tochukwu ne ya shigar da karar, yana zargin cewa wannan tsari ya jefa shi cikin wahalhalu da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa sauya kudin ya karya 'yancinsa na walwala da mutunci a matsayinsa na dan Najeriya mai cikakken ikon.
Dalilin maka Buhari da Emefiele a kotu
Jaridar Punch ta wallafa cewa mai shigar da karar ya shaida wa kotu cewa ya shiga matsanancin hali a lokacin da gwamnatin Buhari ta bullo da tsarin sauya fasalin Naira.
Ya bayyana cewa hakan ya hana shi yawo cikin ‘yanci, kuma bai iya cire kudinsa daga wasu asusun bankuna guda biyu tsakanin watan Janairu da Maris, 2023 ba.

Source: UGC
Tochukwu ya roki kotu da ta ba shi diyya ta Naira biliyan daya saboda take hakkin dan Adam da ya ke zargin an yi masa.
Haka kuma ya nemi kotun ta bayar da umarnin haramta wa gwamnatin tarayya hana amfani da tsofaffin kudade na N200, N500 da N1000.
An kori kara a kan gwamnatin Buhari
Haka zalika, ya bukaci kotu da ta tilasta wa wadanda ake kara su bayar da hakuri a bainar jama’a, tare da wallafa hakan a jaridu biyu manya na kasar nan.
Sai dai a zaman kotun da aka ci gaba da sauraron karar a ranar Litinin, mai shari’a Inyang Ekwo ya yanke hukuncin watsar da karar.
Kotun ta bayyana cewa wanda ya shigar da karar ya kasa bayyana tare da lauyansa ba tare da wani bayani ba.
Lauyan da ke wakiltar Emefiele da CBN, Mista Chikelue Amasiani, ya shaida wa kotu cewa tun bayan shigar da karar a 2023, mai karar da lauyansa suka nuna halin ko in kula a shari'ar.
Saboda haka, ya roki kotu da ta dakatar da ci gaba da sauraron karar, wanda kotu ta amince da hakan tare da rushe karar baki ɗaya.
Buba Galadima ya taso Buhari a gaba
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon makusancin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kuma jigon NNPP, Buba Galadima, ya zazzaga masa ruwan kakkausan suka.
Buba Galadima ya yi zargin cewa tsohon shugaban ƙasan ya ɓoye ainihin halayensa lokacin yakin neman zaɓe, sai da ya hau mulki ya bayyana wa 'yan Najeriya azabar da ke zuciyarsa.
Ya bayyana mamakinsa kan yadda wasu 'yan siyasa ke kai ziyara wurin Muhammadu Buhari, yana mai cewa hakan ba shi da amfani saboda Buhari ya riga ya rasa tasirinsa.
Asali: Legit.ng


