Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Ribadu, Babban Hafsan Tsaro, an Samu Bayanai

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Ribadu, Babban Hafsan Tsaro, an Samu Bayanai

  • Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kira manyan masu muƙamai a fannin tsaro zuwa fadar Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja
  • Bola Tinubu ya shiga ganawa da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da hafsan tsaron, Janar Christopher Musa
  • Ganawar ta su na zuwa ne yayin da matsalolin tsaro suka ƙara taɓarɓarewa a sassa daban-daban na ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, da babban hafsan tsaro na ƙasa, Christopher Musa.

Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da manyan masu muƙaman a fannin tsaron ne a ranar Laraba, 23 ga watan Afirilun 2025.

Tinubu da Nuhu Ribadu
Shugaba Tinubu ya sa labule da Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Bola Tinubu ya kira taro kan rashin tsaro

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ganawar na gudana ne bisa gayyatar shugaban ƙasa, a fadar Aso Rock Villa da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya jajanta kan kashe kashe a Benue, ya fadi shirin Shugaba Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen biyu masu manyan muƙamai sun isa fadar shugaban ƙasan ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana, inda suka shiga ganawa da Shugaba Bola Tinubu a sirrance, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.

Ganawar na zuwa ne yayin da al'amuran tsaro suka ƙara taɓarɓarewa a ƙasar nan.

Al'amuran tsaro sun taɓarɓare a Najeriya

Ƴan bindiga sun kai hare-hare a jihohin Plateau da Benue inda suka hallaka mutane masu tarin yawa.

Hare-haren da ƴan bindigan suka kai, sun jawo asarar rayukan mutane sama da 100 tare da raba wasu da matsugunansu.

Kashe-kashen sun jawo suka da Allah wadai daga mutane da dama a fadin ƙasar nan.

Ƴan adawa sun caccaki shugaban ƙasan kan nuna halin ko in kula da rayukan ƴan Najeriya saboda ci gaba da zamansa da ya yi a ƙasar Faransa lokacin da aka kai hare-haren.

Tinubu ya gana da su Nuhu Ribadu

Kara karanta wannan

Sola a Villa: Bayan sako Tinubu a gaba, fadar shugaban kasa ta buga misali da Amurka

Wannan shi ne karon farko da shugaban ƙasan ke ganawa da manyan hafsoshin tsaro tun bayan dawowarsa daga ƙasashen Faransa da Birtaniya a ranar Litinin.

Shugaban ƙasa ya shafe fiye da makonni biyu a Turai, lamarin da ya jawo maganganu daga wajen ƴan adawa inda suka buƙaci dawowarsa saboda matsalolin tsaro masu tayar da hankali da ke ƙara tsananta.

Sai dai, ba a tabbatar ko sauran hafsoshin tsaro za su samu halartar wannan taro ba a yanzu.

Ana kyautata zaton cewa taron yana da nasaba da tsara sababbin dabaru na fuskantar ƙalubalen tsaro da ƙasar nan ke fama da su.

Gwamnan Benue ya nemi taimakon Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue Hyacinth Alia, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu da ta kai musu ɗauki.

Gwamna Alia ya buƙaci gwamnatin tarayya kan ta tallafawa al'ummar jihar sakamakon matsalar rashin tsaron da suke fama da ita.

Ya nuna cewa a yanzu sun fi buƙatar a taimaka musu maimakon a ƙaƙaba dokar ta ɓaci saboda rashin tsaro a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng