Rashin Tsaro: An Takaita Zirga Zirga a Neja, Za a Ruguza Maboyar 'Yan Ta'adda

Rashin Tsaro: An Takaita Zirga Zirga a Neja, Za a Ruguza Maboyar 'Yan Ta'adda

  • Gwamna Umaru Bago ya sanar da dakatar da zirga-zirgar babura da keke napep daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a Minna saboda tsaro
  • An bayyana cewa matakin zai kasance na ɗan lokaci ne, kuma an cire masu bukatar kulawar lafiya daga cikin waɗanda dokar za ta shafa
  • Gwamnatin jihar ta ce za a rusa gidajen da ake ɓoye ‘yan ta’adda ko ake sayar da miyagun ƙwayoyi, tare da kama duk masu hannu a ciki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Gwamnatin jihar Neja ta sanar da hana zirga-zirgar baburan acaba da Keke Napep daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a cikin birnin Minna, babban birnin jihar.

An bayyana cewa hakan wani yunkuri ne da gwamnatin Umaru Bago ta yi na dakile matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Filato ya fadi wuraren da 'yan bindiga suka mamaye a jiharsa

Umaru
An takaita zirga zirga a Neja kan matsalar tsaro. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan, Balogi Ibrahim ya wallafa a X cewa Umaru Bago ne ya bayyana hakan a taron tsaro tare da hakiman Minna da shugabannin hukumomin tsaro na jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce matakin na ɗan lokaci ne kuma ya shafi birnin Minna kacokan, sai dai an ware masu bukatar kulawar lafiya daga cikin waɗanda dokar ta shafa.

Za a rusa gidajen da ake ɓoye ‘yan ta’adda

Gwamna Bago ya jaddada cewa ba zai zuba ido ya bar miyagu su ci gaba da tada zaune tsaye ba. Ya ce wajibi ne ga kowace gwamnati ta kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Ya gargadi hakimai, dagatai da masu unguwanni da su dinga rubuta bayanan duk wani bako da suka yarda ya zauna a yankunansu.

Gwamnan ya ce za a rushe kowanne gida da aka samu da hannu wajen ɓoye miyagu ko sayar da miyagun ƙwayoyi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun mamaye jihar Benue, Gwamna ya fadi halin da mutanensa suke ciki

Haka zalika, ya bukaci hukumomin tsaro su kutsa cikin mafaka da maboyar miyagu domin kamo su tare da dakile su gaba ɗaya.

Gwamna Bago ya ce za a hukunta masu laifi

Gwamna Bago ya kuma yi gargaɗi ga iyaye da su ja kunnen ‘ya’yansu su guji shiga harkar ta’addanci ko rikici.

Sannan ya ce duk wanda aka kama yana aikata wani ɗanyen aiki na tashin hankali ko fashi za a gurfanar da shi a gaban shari’a.

Ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci harkar ta'addanci ko kyale wasu suna cin karensu babu babbaka ba, tare da tabbatar da cewa doka za ta yi aiki a kan kowa.

Umaru
Gwamnan Neja ya gargadi iyaye da su lura da 'ya'yansu. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Twitter

A cewarsa, tafiyar da mulki aiki ne na kowa da kowa, don haka ya roƙi haɗin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki domin murkushe matsalar rashin tsaro.

Taron dai ya samu halartar mataimakin gwamna Yakubu Garba, Sarkin Minna Alhaji Umar Faruk Bahago, da dagatai da jami’an tsaron jihar.

Tinubu zai gana da shugabannin tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai gana da shugabannin tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ba mu buƙatar albarkar shi kafin fatattakar Tinubu," Tsohon Sakataren gwamnatin Buhari

Hakan na zuwa ne bayan Bola Tinubu ya dawo daga Faransa a wata ziyarar aiki da ya kai zuwa kasashe Turai.

Tun yana hutu a Turai aka matsa lamba ya dawo Najeriya domin fuskantar kalubalen tsaro da ya dabaibaye wasu jihohin kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng