Bayan Kashe Mutane, ana Zargin An Saka wa Shanu 32 Guba a Filato
- Sojojin Operation Safe Haven sun dakile yunkurin ramuwar gayya bayan gano shanu 32 da suka mutu a yankin Bassa da aka kashe mutane
- Rahotanni sun nuna cewa shanun sun nuna alamun mutuwa bayan sun yi kiwo a wani fili da ake zargin an zuba kayan lambu masu guba
- Gwamnatin jihar Filato ta aika da likitocin dabbobi da masu bincike don gano gaskiyar lamarin, tare da yin kira ga jama’a da su guji rikici
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - Sojojin Operation Safe Haven (OPSH) sun gaggauta kai dauki bayan bullar rahoton sanya wa shanu 32 guba a yankin karamar hukumar Bassa da ke Jihar Filato.
Rahotanni sun bayyana cewa shanun mallakin wani makiyayi mai suna Samaila Nuhu ne, inda suka mutu bayan sun ci abinci a wani fili a tsakanin Dutsen Kura da Jebbu Miango.

Source: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa dama yankin ya dade yana fama da rikicin manoma da makiyaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyin sojoji sun ce makiyayin ya lura da canji a lafiyar dabbobinsa, abin da ya sa ya zargi an basu guba, sai dai sojojin OPSH sun isa wurin bayan samun kiran gaggawa.
An yanka shanun da ake zargi sun ci guba
Sojojin da suka kai samame sun tabbatar da cewa makiyayan sun yanka shanun da suka kamu da ciwon don ceto naman da za a iya amfani da shi.
Binciken farko da aka yi ya gano cewa akwai tumatur da ganyen gauta da ake kyautata zaton suna dauke da guba a wajen.
Babu wata mafaka ko gida a kusa da wurin, wanda hakan ke nuna yiwuwar wasu sun jefar da guban da gangan domin cutar da dabbobin.
Don dakile tasirin rikicin, Kwamandan OPSH ya jagoranci tawagar manyan jami’ai ciki har da shugaban karamar hukumar Bassa, ‘yan sanda da sauran shugabanni zuwa wajen.
Gwamnati da 'yan sanda sun shiga lamarin
Kakakin ‘yan sandan Filato, Alfred Alabo, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce DIG Bzigu Kwazhi da kwamishinan ‘yan sanda, Emmanuel Adesina, sun ziyarci wajen domin jaje.
Kwamishiniyar yada labarai da sadarwa ta jihar, Joyce Ramnap, ta bukaci jama’a da su yi hattara da yada jita-jita.
Vanguard ta wallafa cewa Joyce Ramnap ta ce kwararru daga fannin kiwon lafiya da muhalli sun fara daukar samfur don tantance gaskiyar lamarin.

Source: Facebook
Gwamnati ta bukaci a kwantar da hankali
Ramnap ta jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kokari wajen inganta zaman lafiya da warware matsalolin filaye da kiwo ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.
Shugaban karamar hukumar Bassa, Joshua Riti, ya bayyana bakin ciki bisa faruwar lamarin, tare da yin kira ga daukacin bangarorin da su zauna lafiya su bar hukumomi su gudanar da bincike.
An saka sababbin dokoki a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Filato ta sanya sababbin dokoki domin dakile rikice-rikice.
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana cewa daga ranar Larabar da ta wuce an hana kiwon shanu da dare a jihar.
Baya ga haka, gwamnan ya bayyana cewa an takaita zirga zirgar abubuwan hawa, musamman babura domin hana tayar da rikici.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


