Tsufa Ya Zo da Gardama: Dattijo Ɗan Shekara 50 Ya Ɗirka wa Ƴarsa Ciki a Bauchi
- Wani dattijo dan shekaru 50, Umar Sule, ya shiga hannun ‘yan sanda bisa zargin dirka wa ’yarsa mai shekaru 17 ciki a jihar Bauchi
- Lamarin ya faru ne a Kurmin Ado, karamar hukumar Ganjuwa, inda wanda ake zargi ya amsa cewa ya yi lalata da 'yarsa babu adadi
- Jami’an tsaro na ci gaba da bincike yayin da kwamishinan ‘yan sanda ya bayar da umarnin gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Rundunar 'yan sanda ta kama wani dattijo dan shekara 50 mai suna Umar Sule kan zarginsa da dirka wa 'yarsa ciki a Bauchi.
Lamarin ya faru ne a kauyen Kurmin Ado da ke karkashin gundumar Kariya a karamar hukumar Ganjuwa, jihar Bauchi, kamar yadda rundunar 'yan sanda ta tabbatar.

Asali: Twitter
An cafke dattijo kan lalata da 'yarsa a Bauchi
Kakakin rundunar na Bauchi, CSP Ahmed Wakili, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa menam labarai, inji rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa CSP Ahmed Wakili:
“A ranar 3 ga Afrilu, 2025, misalin karfe 4:30 na yamma, rundunar 'yan sandan Bauchi ta samu korafi daga wani mai suna Abdullahi Baban Karatu.
“Wanda ya kai korafin dan Kurmin Ado ne, kuma ya zargi wani mai suna Umar Sule, mai shekaru 50, da aikata wannan mummunan laifi.”
Jaridar Punch ta rahoto ASP Wakili ya kara da cewa:
“An ce a watan Nuwambar shekarar 2024, Umar ya yi lalata da 'yarsa a dakin matarsa a lokuta daban-daban cikin dare.”
Bauchi: Yadda mahaifi ya dirka wa 'yarsa ciki
Bayan karɓar wannan rahoto, rundunar ta tura wata tawaga ta kwararrun jami’ai domin bincike da kuma kama wanda ake zargi da aikata laifin.
A yayin binciken, wanda ake zargin ya amsa laifinsa a fili, yana mai cewa ya sadu da 'yarsa ba sau daya ko biyu ba, har ta samu ciki.

Kara karanta wannan
Portable: Ƴan sanda sun kama fitaccen mawakin Najeriya, an ji laifin da ya aikata
A cewar rahoton wani kwararren likita, an tabbatar cewa yarinyar tana dauke da juna biyu na wata uku sakamakon cin zarafin da mahaifinta ya yi.
A yayin hira da yarinyar, ta tabbatar da cewa mahaifinta ne ke lalata da ita, kuma hakan ya faru ne lokacin da mahaifiyarta ba ta gari, ta yi tafiya.
Ta ce mahaifiyarta ta je ziyara wurin iyayenta a kauyen Burra, karamar hukumar Ningi, lokacin da mahaifinta ya fara amfani da damar yana lalata da ita.
'Yan sanda za su gurfanar da dattijo gaban kotu

Asali: Original
Bayan dawowar mahaifiyarta daga tafiya, ta lura da canjin yanayi a jikin yarinyar, inda ta yi mata tambayoyi, har dai daga bisani ta fada mata cewa mahaifinta ne ya yi mata cikin.
Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa tana ci gaba da bincike, kuma za a mika lamarin zuwa kotu da zarar an kammala binciken.
Sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarni cewa a gurfanar da wanda ake zargi a kotu bayan kammala bincike.
An kama wanda ya yi wa yarsa ciki a Adamawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar ƴan sandan Adamawa ta kama wani magidanci da ake zargi da lalata da ƴar cikinsa har ta samu juna biyu.
'Yan sanda sun ce wanda ake zargin, Matthew Joseph ya fara lalata da yarsa ne bayan ya saki mahaifiyarta kimanin shekara guda.
Binciken da rundunar ta gudanar ya nuna wacce abin ya faru da ita tana dauke da juna biyu na watanni uku kamar yadda likitocin da suka duba ta suka tabbatar.
Asali: Legit.ng