An kama wani mutum da ya yi wa 'yarsa ciki a Adamawa

An kama wani mutum da ya yi wa 'yarsa ciki a Adamawa

– Ƴan sanda sun kama wani magidanci, Matthew Joseph, a jihar Yola bisa zarginsa da yi wa diyar cikinsa ciki

– Matthew Joseph mai shekara 42 ya fara lalata da yarsa mai shekara 17 ne bayan ya saki mahaifiyarta

– Binciken da yan sanda suka gudanar a halin yanzu ya nuna yarinyar tana da juna biyu na wata uku kuma likitoci na cigaba da duba ta

Rundunar ƴan Sandan Jihar Adamawa ta kama wani magidanci mai shekaru 42 da ake zargi da lalata da ƴar cikinsa mai shekaru 17 har da lamarin ya kai ta samu juna biyu.

Kakakin rundunar ƴan Sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Alhamis a Yola.

Nguroje ya ce kama magidanci da rundunar ta yi wani nasara ne da suke samu wurin yaƙi da fyade a jihar.

Mahaifi ya dirka wa diyarsa ciki a Adamawa
Mahaifi ya dirka wa diyarsa ciki a Adamawa. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Mata mai juna biyu ta datse mazakutar mijinta da wuka a Taraba

"Yan sanda na samun nasara a yakin da masu fyade da cin zarafin mata da yara a jihar.

"Rundunar a ranar 1 ga watan Yuli ta kama wani mutum mai shekara 42, Matthew Joseph, mazaunin karamar hukumar Yola ta Kudu kan yin lalata da yarsa mai shekara 17.

"Wanda ake zargin ya fara lalata da yarsa ne bayan ya saki mahaifiyarta kimanin shekara guda kuma ya rika lalata da ita har sai da ta samu juna biyu.

"Binciken da aka gudanar kawo yanzu ya nuna wacce abin ya faru da ita tana dauke da juna biyu na watanni uku kuma likitoci suna duba ta," in ji Nguroje.

Yace rundunar yan sandan ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin ladabtar da duk wanda aka samu da laifi a lamarin.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa yan sandan sun kuma yi holen wasu mutum 23 da ake zargi da fyade da luwadi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel