Aikin Assha: Wani Uba ya yiwa ‘yarsa mai shekaru 15 ciki

Aikin Assha: Wani Uba ya yiwa ‘yarsa mai shekaru 15 ciki

- Yawaitar yiwa yara kanana fyade na dada ta'azzara

- Wani Uba da ake zargi da yiwa 'yarsa cikin shege ya ki amincewa da aikata laifin a kotu

‘Yan sanda sun gurfanar da Mutuma mai suna Samaila Zakari mai shekaru 50 gaban kotun majistire a jihar Gombe bisa zargin dirkawa ‘yarsa cikin shege.

Rahotan da ‘yan sanda suka gabatar a kotun ya nuna cewa, Mutumin da ake zargi mazaunin garin Deba ya aikata laifin ne ranar 2 da kuma 8 ga watan Mayun da ya gabata, da misalin ƙarfe 10pm na dare yayi lalata da ita ba tare da sanin ta ba.

Aikin assha: Wani Uba yayiwa ‘yarsa mai shekaru 15 ciki
Aikin assha: Wani Uba yayiwa ‘yarsa mai shekaru 15 ciki

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya shaidawa kotun cewa yanzu haka ‘yar Sama’ilan na ɗauke da juna biyun da yayi mata na watanni biyu.

KU KARANTA: Allah yayi: Kotu ta bayar da belin Dino Melaye kan wasu makuden miliyoyi

Wanda ake zargin da aikata laifin yayi amfani da wayo wajen yi wa yarinyar fyaɗe wanda hakan laifi ne da ya saɓawa sashi na 390 da kuma 282 na kundin shari’a. A cewar 'Dan sandan.

Amma sai dai ana shi ɓarin, wanda ake zargi Samaila Zakari ya musanta aikata laifin.

Bisa wannan dalili ne Ɗan sanda mai gabatar da kara ya bukaci da a ɗage shari’ar domin basu damar zurfafa bincike.

Nan take mai shari’a Mr Dorabo Sikam ya karɓi buƙatar hakan, kana ya ɗage shari’ar zuwa 21 ga watan Mayu domin cigaba da sauraron ƙarar sannan ya sanya a tisa keyar wanda ake zargin zuwa gidan Maza.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng