A kama fasto da ya ɗirka wa ƴar cikinsa juna biyu har sau uku

A kama fasto da ya ɗirka wa ƴar cikinsa juna biyu har sau uku

- 'Yan sanda sun damke wani fasto mai shekara 44 da ya rika yi wa yar cikinsa fyade bayan rasuwar mahaifiyarta

- Faston mai suna Oluwafemi Oyebola ya rika lalata da yarsa ne tun shekarar 2015 a lokacin shekarar ta 19

- Ya yi wa yarsa ciki har sau uku yana zubarwa hakan yasa yar ta yi kararsa wurin yan sanda kuma aka kama shi

A kama fasto da ya ɗirka wa ƴar cikinsa juna biyu har sau uku
Oluwafemi Oyebola. Hoto daga LIB
Asali: UGC

'Yan sanda a jihar Ogun sun kama wani faston cocin Christ Apostolic Church (CAC) a yankin Ogo Oluwa, mai suna Oluwafemi Oyebola da ake zargi da yi wa yar cikinsa fyade.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kama faston ne bayan 'yarsa ta shigar da rahoto a hedkwatar 'yan sanda da ke Owode-Egbado.

Sanarwar da kakakin 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ta fitar ya bayyana cewa yarinyar ta ce mahaifinta ya fara tilasta mata yin lalata da shi ne tun shekarar 2015 a lokacin shekarun ta 19 jim kadan bayan rasuwar mahaifiyarta.

A cewar ta, sau uku mahaifin nata yana yi mata ciki kuma yana kai ta ta wurin wata maaikacciyar asibiti ana zubar da cikin.

Oyeyemi ya ce, "bayan an zubar mata da cikin na uku, wanda ake zargin ya yi mata tsarin kayyade iyali domin kada ta sake samun juna biyun."

"Yayin da ta lura cewa mahaifinta zai lalata mata rayuwa, ta tsere daga gida ta kai rahoto zuwa kungiya mai zaman kanta, ‘‘Advocacy For Children And Vulnerable Persons Network’’ daga nan kuma suka kai ta ofishin yan sanda da ke Owode-Egbado."

DUBA WANNAN: An kama shugaban kungiyar miyagu ta Shila a Adamawa

Kakakin yan sandan ya ce bayan samun rahoto, DPO na Owode-Egbado, SP Olabisi Elebute ya dauki yan sanda sun tafi gidan faston inda suka kama shi nan take.

Ya cigaba da cewa, "A yayin da aka masa tambayoyi, wanda ake zargin ya tabbatar da cewa dukkan abinda yarsa ta fadi gaskiya ne."

Oyeyemi ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Kenneth Ebrimson ya bayar da umurnin mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken masu yaki da safarar mutane da cin zarafin yara a karkashin sashin binciken manyan laifuka, CID.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel