Zaben 2027: An Ji Dalilin 'Yan Siyasa na Tururuwar Kai wa Buhari Ziyara a Kaduna

Zaben 2027: An Ji Dalilin 'Yan Siyasa na Tururuwar Kai wa Buhari Ziyara a Kaduna

  • Yayin da 2027 ke kara karatowa, ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban na kai ziyara gidan Muhammadu Buhari domin neman goyon bayansa
  • Ziyarar Atiku Abubakar zuwa wurin Buhari ta janyo cece-kuce, yayin da APC ke kokarin hana tsohon shugaban janye wa daga jam’iyyar
  • Masu sharhi na ganin Buhari zai yi tasiri a 2027 musamman a Arewa, wanda ya sa APC da jam'iyyun adawa ke neman goyon bayansa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Yayin da ya rage saura shekaru babban zaben 2027, an fara ganin yadda ‘yan siyasa ke kai wa da komowa gidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ganin yadda ‘yan siyasa daga APC da kuma ‘yan adawa ke tururuwar zuwa gidan Buhari a Kaduna don ganawa da shi da daukar hotuna ya janyo ce-ce-ku-ce daga 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Abin ya fara damun Tinubu, an 'gano' shirinsa kan ƴan APC da ke son komawa SDP

Masana sun yi sharhi kan yadda 'yan siyasa ke tururuwar zuwa gidan Buhari a Kaduna
Abin da masana suka ce kan yadda 'yan siyasa ke tururuwar zuwa gidan Buhari a Kaduna. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

A cewar rahoton jaridar Daily Trust, wadannan ziyarce-ziyarce da 'yan siyasa ke kai wa Buhari, na nuni da wani babban al'amari na siyasa da ke gudana a bayan fage.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya sake zama mai tasiri a siyasar Najeriya

Buhari wanda ake ganin ya nisanci siyasa bayan barin ofis, yanzu yana ci gaba da zama wani ginshiki ga 'yan siyasa da ke neman mukamai a 2027.

Ana ganin cewa, dukkanin masu kai wa Buhari ziyara, na neman amincewarsa, goyon baya ko a kalla rashin nuna kin jini daga gare shi gabanin zaben.

Canjin jam’iyya da Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna, ya yi zuwa SDP ya kara hura wutar rade-radin yadda Buhari ke kara tasiri a siyasa a yanzu.

Don haka ne lokacin da Atiku Abubakar ya kai ziyarar Sallah tare da wasu fitattun ‘yan siyasa irinsu El-Rufai da Aminu Tambuwal zuwa gidan Buhari.

Kara karanta wannan

Bayan ganawarsu, an tono bidiyo da Ganduje ke sukar Buhari kafin zaben Tinubu

Da dama daga cikin masu sharhi sun dauki hakan a matsayin kokarin janyo tsohon shugaban cikin tafiyarsu.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin abokan tafiyar Buhari a tsohuwar jam’iyyar CPC na shirin ficewa daga APC, saboda wariyar da ake nuna masu.

Kodayake Atiku ya musanta cewa tattaunawar siyasa ce aka yi da Buhari, amma El-Rufai ya kara tada kura da wani sakon barkwanci da ya wallafa a kafar sada zumunta bayan ganawar.

El-Rufai ya wallafa a shafinsa na X cewa:

“Kada ziyararmu ta hana makiyanmu barci. Ba siyasa muka zo ba. Mun zo sada zumunci ne. Kuma tunda ba mu da amfani, mun zo ne mu yi addu’a da cin abinci tare da na-gaba-da-mu.”

APC ta kai ziyara gidan Buhari bayan Atiku

Ziyarar da gwamnonin APC suka kai wa Buhari kafin ta Atiku, da kuma ziyara shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje, da kwamitinsa bayan tafiyar Atiku ya kara tayar da jijiyoyin wuya.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume na shirin ficewa daga APC ya haɗe da El Rufai a SDP? Ya yi bayani da bakinsa

Bayan ganawar, Ganduje ya rage tasirin ziyarar Atiku, amma hakan ya sa wasu suka fahimci cewa APC na kokarin tabbatar da cewa Buhari bai janye hannunsa daga jam’iyyar ba.

Ana ganin hakan na faruwa ne a daidai lokacin da adawa ke samun karbuwa musamman a Arewacin Najeriya inda ake adawa da salon mulkin Bola Tinubu.

Siyasar tsoro ko yakin jawo goyon bayan Arewa?

Masanin siyasa Shamsudeen Ibrahim ya ce ziyarar Ganduje da kwamitinsa zuwa wurin Buhari na nuna tsoron jam’iyyar, tsoron rasa Arewa da kuma tsoron rugujewar turakun jam’iyyar.

Shamsudeen ya kara da cewa:

“Yanzu haka APC na kallon Buhari kamar wani ginshikin samun nasara duk da sun rika nesanta kansu daga manufofinsa a baya.
"Siyasa a Najeriya ba ta da tabbas – da zarar mutum bai da amfani, sai a juya masa baya. Amma idan ya sake zama tauraro, sai a sake komawa gare shi.”

A cewarsa, siyasar Najeriya na da tarihi na mantawa da abubuwa da wuri. Kuma yanzu, Buhari ya sake zama mai tasiri da 'yan siyasar kowanne bangare ke nema.

Kara karanta wannan

Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

Dalilin da ya sa ‘yan adawa ke neman Buhari

Umar Sani, daya daga cikin jiga-jigan PDP ya ce hadakar da Atiku ke jagoranta na bukatar Buhari ta hanyoyi da dama.

Umar ya ce:

“Suna da bukatarsa domin ya fitar da ragowar 'yan CPC daga APC. Hakan zai raunana jam’iyyar mai mulki. Kuma har yanzu Buhari shi ne mafi farin jini a Arewa.”

Ya kara da cewa duk da wasu na ganin Buhari ya rasa farin jini, har yanzu yana da tasiri sosai a siyasar Arewa.

“Wasu na ganin idan Buhari ya goyi bayan wani dan takara, zai samu kuri’u a wuraren da ba su taba goyon bayan wata jam’iyya ba.”

- Inji Umar.

Buhari da tasirinsa na kuri’u miliyan 12

A cewar Umar Sani, APC na kokarin tunatar da Buhari irin sadaukarwar da suka yi masa domin ya zama shugaban kasa a 2015 da 2019.

Ganin yadda Buhari ya koma Kaduna daga Daura, ake hasashen cewa yana da burin dawowa cikin harkar siyasa sosai.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku da El Rufa'i, Ganduje ya dura gidan Buhari da jiga jigan APC

An tambaye shi ko hakan na nuna canjin cibiyar karfin siyasa daga Minna zuwa Kaduna, Umar Sani ya ce:

“Buhari shi ne shugaban soja na farko daga Arewa da ya lashe zabe sau biyu karkashin tsarin dimokradiyya.”

Sani ya kara da cewa Buhari ya taba samun kuri’u miliyan 12 a kusan duk zabukan da ya tsaya – sai a 2007 da ya yi rashin nasara, inda marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya lashe zaben.

“Yanzu mutane na ganin Buhari na iya tabbatar da samun kuri’u a Arewa. Duk wanda ya samu amincewarsa a 2027 zai iya samun kuri'u sosai,” inji Umar.

Sai dai a zaben 2023, wasu sun fara shakkar karfin wannan “kuri'u miliyan 12” din, domin Bola Tinubu bai samu sama da kuri’u miliyan takwas ba.

Wa Buhari zai goya wa baya a 2027?

Masana sun magantu kan wanda Buhari zai iya marawa baya a 2027
An ji yadda 'yan siyasa ke neman amincewar Buhari gabanin zaben 2027. Hoto: @atiku, @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Dr Saidu Dukawa na jami’ar BUK ya ce wadannan ziyarorin da ake kai wa Buhari sun nuna cewa an fara shirin zaben 2027 tun yanzu.

Kara karanta wannan

"Ni ma zan lallaɓa," Ndume ya faɗi dalilin da ya sa manyan ƴan siyasa ke zuwa wurin Buhari

Malamin jami'ar ya shaida cewa:

“Za a kai irin wadannan ziyarorin zuwa ga Olusegun Obasanjo da Goodluk Jonathan nan gaba. Amma abin da ke bayan fage zai bayyana ne daga baya.”

Dr Sam Amadi, daraktan makarantar nazarin siyasa ta Abuja ya ce:

“Buhari bai taba nuna zai jagoranci wani yunkuri ko jam'iyyar siyasa ba matukar ba shi zai amfana da hakan kai tsaye ba.
“Dukkanin jam’iyyu na kokarin janyo Buhari ne saboda sun san cewa kuri’un Arewa ne za su yanke wanda zai ci zabe a 2027. Amma la'akari da salon siyasar Buhari, yana iya kin bayyana wanda zai goyi baya kai tsaye.”

'Yan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

Tun da fari, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar ya jagoranci tawaga mai ƙarfi zuwa gidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kadun.

Duk da cewa ba a samu cikakkun bayanai ba, amma Atiku ya bayyana ziyarar a matsayin gaisuwar Sallah da kuma nuna girmama ga Buhari.

Daga cikin waɗanda suka raka shi akwai fitattun mutane irinsu tsoffin ministoci, gwamnoni da manyan masu riƙe da muƙamai, ciki har da Nasir El-Rufai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng