Abin Al'ajabi: Wata Yarinya da Aka Yi Jana’izarta a Kano Ta Dawo Gida da Ranta
- An shiga rudani a jihar Kano yayin da aka ce wata yarinya da ta rasu kuma aka birne ta a Ramadan din da ya wuce, ta dawo gida da ranta
- Wani Kwamared Usama Lere ya ce ya je garin Kura domin tabbatar da gaskiyar batun, inda ya tarar da mutane suna tururuwar ganin yarinyar
- Wannan batu ya jawo martanin jama'a sosai, inda wasu ke ganin cewa ba ita ce aka binne ba, yayin da wasu ke ganin lamarin karya ne kawai
- A zantawar mu da Gwani Abubakar Sa'iddu, kan ko addinance irin hakan za ta iya faruwa, ya ce tunanin hakan ma babban laifi ne
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Mutane sun shiga tsananin rudani a jihar Kano da aka samu labarin cewa wata yarinya da aka yi jana'izarta ta dawo gida da ranta.
Wannan al'amari da ya faru, da wasu ke misalta shi da 'almara' ya ja hankalin mutane sosai, inda aka rika tururuwar zuwa ganin yarinyar a gidansu.

Asali: Original
Yarinyar da ta rasu a Kano ta dawo gida da rai
Wani matashi mai suna Kwamared Usama Lere Kura, da ya aika sako ga gidan rediyon Freedom Kano a ranar 9 ga Afrilu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sakon da ya aika, Kwamared Usama ya ce da fari shi ma labari a ka kai masa, cewa wata yarinya ta rasu a cikin azumi, amma kuma ta dawo gida da ranta.
Saboda rashin yarda da wannan labari da aka ba shi, Kwamared Usama ya ce ya garzaya unguwar da aka ce abin ya faru, inda ya tarar da cunkoson mutane.
Mutane na zuwa ganin yarinyar da 'ta mutu ta dawo'
Kwamared Usama ya ce kofar gidansu yarinyar na a cike, mutane na shiga suna ganinta, lamarin da ya kara rikita tunanin mutane a kan ko 'ta mutu ta dawo ne.'
Ya ce ko da ya ga yarinyar, ga ta gabansa, da ranta, sai ya cika da tsananin mamaki, domin a cewarsa, yana kallon abin ne kamar a fim.
Matashin ya ce wannan abin al'ajabi ya faru ne a garin Alkalawa da ke cikin karamar hukumar Kura, jihar Kano, kuma har yanzu mutane na tururuwar zuwa ganin yarinyar.
Mutane sun yi martani kan wannan abin al'ajabi

Asali: UGC
Legit Hausa ta tattaro kadan daga cikin ra'ayoyin jama'a kan wannan abin al'ajabi da ya faru a Kano.
Ãbubakar Yusuf:
"Gaskiyar abin da ya faru a karamar hukumar Kura.
"Ita wanan baiwar Allah da azumi ta bata ba a ganta ba sai daga baya aka samu labarin wai ta mutu, an tsinci gawarta, wai har an binneta, sai yau kuma aka ganta.
"To gaskiyar zance shi ne, gawar da aka binne ba ta ta ba ce, domin da kaya ta dawo gida ba likkafani ba.
"Na biyu shi ne ba ita aka binne ba, saboda ba wanda zai iya ba ka tabbaci a kan yadda aka yi janaizarta, Allah ka sa mu dace."
Umar Sa'eed Mai Waka:
"Ba ita ce ta mutu ba wallahi, ko labarin kanzon kurege babu inda aka mutu aka dawo."
Alh Musa Shuaibu:
"Kai tun da ake mutuwa ake binne mutane ka taba samun labarin wanda ya dawo ko kuma ya aiko sako? To gaskiya ku daure ku dinga yada gaskiya saboda gudun rudani. Allah ya kyauta."
Murtala Ya'u Ibrahim:
"Daman ba ita ta mutu ba, domin babu wanda zai mutu kuma ya dawo. Ba mu taba ji ba balle gani, a dai kara bincike."
Abubabakar Nasir Danmaliki:
"In da ranka ka sha kallo, Allah ya sa mu dace.'
Abdulaziz Lawan Sadauki:
"Hakan ba zai taba faruwa ba, idan za ta faru kuma akan annabawan Allah za ta faru, a mutu kuma a tashi, kai! Ba zai yiwu ba, sai dai idan wani abu akayi ba mutuwa ba, amma mutuwa daya ce bata da na biyu."
Usman Ibrahim Doro Doro:
"Karya ce kawai, babu wanda ya isa ya mutu kuma ya dawo. Babu shi walllahi."
'A guji tsallake iyakokin Allah' - Gwani Abubakar
A zantawar mu da Gwani Abubakar Liman Sa'iddu, kan ko addinance irin hakan za ta iya faruwa, ya ce tunanin hakan ma babban laifi ne.
Gwani Abubakar ya gargadi masu yada irin wannan ''barnar" da su kiyayi yin wasa da abin da Allah ya yi wa iyaka.
"Ka ce wai wata ko wani ya mutu ya dawo, kuma har ka gasgata hakan, babban laifi ne, domin ka karyata abin da Allah ya ce, da kuma sakon da Annabi ya da shi.
"Idan da ace wani zai mutu ya dawo, kuma ya ci gaba da rayuwa, to da Annabi ne za a ba wannan dama, amma shi ma ya rasu, kuma sama da shekaru 1446, bai dawo ba.
"Mu kiyayi kanmu daga ire-iren waɗannan batutuwan. Duk abin da aka ce Allah ya yi togaciya a kansa, to mu kiyaye tsallaka iyaka."
'Yar shekara 12 ta farfado ana jana'izarta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata yarinya ‘yar shekara 12 da aka tabbatar da rasuwarta ta dawo da ranta a lokacin da ake shirin kai ta makwanci.
An ce ta farfaɗo ne bayan awa guda da likita ya tabbatar da mutuwarta a asibiti, amma jim kaɗan bayan haka, sai kuma ta sake riga mu gidan gaskiya.
Lamarin ya faru a kasar Indonesiya ne, inda shugaban rundunar 'yan sandan yankin ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng