Abun mamaki: Hotunan yarinya ƴar firamare tana gyaran motoci ya jawo cece kuce a yanar Gizo

Abun mamaki: Hotunan yarinya ƴar firamare tana gyaran motoci ya jawo cece kuce a yanar Gizo

- Wani mai amfani da shafin Twitter @AD_Kwatu ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan Najeriya bayan wallafa hotunan wata yarinya da ke gyara motoci

- An tattaro cewa yarinyar yar makarantar firamare da aka bayyana da suna Khadija tana gyara birkin mota yayinda take zuwa makaranta

- Mutane da dama sun nuna mamakin yadda ta sadaukar da kan ta ga aiki, wasu kuma sun yi korafin cewa aikin makanike zai shafi rayuwarta ta yarinta

Wata yarinya 'yar makarantar firamare ta haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan hotunanta sun bayyana inda take gyaran motoci.

Da ya wallafa labarin a shafin Twitter tare da hotunan ta a bakin aiki, @AD_Kwatu ya ce yarinyar da aka bayyana da suna Khadija ta kasance mai gyaran motoci wacce ta kware wajen gyaran birki kuma har yanzu tana zuwa makaranta duk da aikin ta.

KU KARANTA KUMA: Gumi ya koma limamin ƴan bindiga, ya kamata a tuhume shi, cewar wata ƙungiyar Arewa

Abun mamaki: Hotunan yarinya ƴar firamare tana gyaran motoci ya jawo cece kuce a yanar Gizo
Abun mamaki: Hotunan yarinya ƴar firamare tana gyaran motoci ya jawo cece kuce a yanar Gizo Hoto: @AD_Kwatu
Asali: Twitter

Ya wallafa:

"Haɗu da Khadija!!" Dalibar makarantar firamare wacce ta kware wajen gyara birkin mota. Ta fito daga Paiko, jihar Neja. Ba ta yin talla, tana zuwa makaranta kuma tana da kwazo wurin aiki."

KU KARANTA KUMA: Bankwanan ADC da Buhari: Ƙaramar yarinya ta nuna bajinta, ta sarawa shugaban ƙasa

Wallafar ya samu sharhi kala-kala daga ‘yan Najeriya. Yayin da wasu ke yabawa yarinyar don sadaukar da kai ga aikinta, wasu kuma na ganin ta yi kankanta da gyaran motoci.

@UmarKani ya ce:

"Abun takaici da kyama shine cewa irin wannan na faruwa a Arewa ... wannan ya nuna karara bambanci tsakanin iyayen wannan zamanin da kakannin mu."

@bwidufu ya rubuta:

"Na yi mamakin sadaukarwar ta duk da cewa abin takaici ne matuka cewa ba ta ci moriyar yarintarta ba."

@abbatee_61340 yayi sharhi:

"@CaptJamyl kila ka so ganin wannan kuma albarkar da rahama na iya zuwa ta wurin ka."

@binta_rasul ta mayar da martani:

"Na taba haɗuwa da ita sau ɗaya a kan hanyata ta zuwa Abuja daga Minna. karamar yarinya mai wayo sosai."

A wani labarin, an kori wata 'yar Najeriya a ranar farko da ta fara aiki bayan ta tambayi manajan nata idan 'zata samu damar kebewa da shi kuma za ta iya zama a fuskarsa' a ranartata farko a wajen aiki.

Jagoran ci gaban kamfanin Dipo Awojide ne ya bayyana hakan a shafin soshiyal midiya.

A cewar Awojide, za a biya matar da ake magana a kanta kudin aiki na kwana daya bayan an kore ta. Ya kuma bayyana cewa kamfaninsa zai tallata aikin yarinyar nan ba da dadewa ba.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel