Yarinyar 'yar shekara 12 da ta mutu ta dawo a yayin da ake shirin jana'izarta

Yarinyar 'yar shekara 12 da ta mutu ta dawo a yayin da ake shirin jana'izarta

- Rahotanni sun nuna wata yarinya 'yar shekara 12 da ta mutu ta dawo duniya a daidai lokacin da ake yi mata wanka za a kai ta makwanci

- Yarinyar ta dawo awanni kadan bayan mutuwa a asibiti, sai dai kuma bayan shafe kimanin awa daya da mutuwa ta sake mutuwa

- Lamarin ya faru a kasar Indonesiya ne, inda shugaban rundunar 'yan sandan yankin ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai

Wata yarinya 'yar shekara 12 ta dawo duniya a daidai lokacin da danginta ke shirin binneta.

Yarinyar mai suna Siti Mastufah Wardah, an kai ta asibiti a Probolinggo dake Gabashin jihar Java a cikin kasar Indonesia, sakamakon wani ciwo da ya kamata a ranar 18 ga watan Agusta. An bayyana cewa ta mutu da misalin karfe 6 na yamma.

Yarinyar 'yar shekara 12 da ta mutu ta dawo a yayin da ake shirin jana'izarta
Yarinyar 'yar shekara 12 da ta mutu ta dawo a yayin da ake shirin jana'izarta
Asali: Facebook

An kai gawarta ga danginta domin su yi mata sallah kamar yadda addinin Musulunci ya tsara.

Amma a daidai lokacin da ake yi mata wanka, sai kawai gani aka yi idon Siti ya bude cikin ikon Allah sai ta tashi.

Mahaifinta mai suna Ngasiyo, mai shekaru 40 ya bayyana halin da ya shiga bayan diyar tashi ta dawo.

"A lokacin da ake yi mata wanka sai yanayin jikinta yayi zafi," ya sanar da manema labarai.

"Sai idonta ya bude. Sai muka ji zuciyarta tana bugawa kuma jikinta yana motsi."

KU KARANTA: Tashin hankali: Sojoji sun kashe sufeto na 'yan sanda da duka a Najeriya

An kira likitoci wajen inda suka bawa Siti taimakon gaggawa da zai taimaka mata tayi numfashi da kyau.

Sai dai kuma bata jima da dawo ba sai Allah ya kara karbar abarsa. Daga nan aka yi mata wanka aka binne ta a makabarta.

Yarinyar 'yar shekara 12 da ta mutu ta dawo a yayin da ake shirin jana'izarta
Yarinyar 'yar shekara 12 da ta mutu ta dawo a yayin da ake shirin jana'izarta
Asali: Facebook

Shugaban rundunar 'yan sanda na Lumbang, Cif AKP Muhammad Dugel ya tabbatar da faruwar lamarin bayan ya kai ziyara wajen da lamarin ya faru.

"Kwarai da gaske ne wannan lamari ya faru, yarinyar ta mutu ta dawo, bayan an kwantar da ita a asibiti," ya sanar da manema labarai.

"A lokacin da ake yi mata wanka ta dawo tana motsi bayan shafe kimanin awa daya, sai ta sake mutuwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel