Daga karshe, Kotu Ta Yi Zama kan Shari'ar Kisan Gilla da Aka Yi Wa Janar Alkali a Jos

Daga karshe, Kotu Ta Yi Zama kan Shari'ar Kisan Gilla da Aka Yi Wa Janar Alkali a Jos

  • Kotu da ke zamanta a Jos ta dage shari’ar da ake yi kan kisan Janar Idris Alkali zuwa 28 da 29 ga watan Mayu, 2025
  • An tabbatar da cewa masu kare kansu a karar za su fara gabatar da shaidu domin wanke kan su daga wannan tuhuma
  • Lauyan masu kare kai ya yi tambayoyi masu yawa ga Janar Mohammed game da bincikensa wanda ya dauki tsawon lokaci
  • Alƙalin kotun da ya saurari shari'ar, Arum Ashom bai samu wani ƙalubale daga masu ƙara ba kan dage sauraran shari'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Babbar kotu da ke Jos, Jihar Plateau ta saurari karar da aka shigar saboda kisan Manjo-Janar Idris Alkali a Jos.

Kotun ta sake dage shari’ar kisan tsohon sojan zuwa karshen watan Mayun shekarar 2025 domin ci gaba da kokarin gano gaskiya.

Kara karanta wannan

An bayyana shirin Atiku da Obi na haduwa da El Rufa'i a SDP domin kifar da Tinubu

Kotu ta zama kan shari'ar kisan Janar Alkali a Jos
Kotu ta dage shari'ar kisan gilla da aka yi wa Janar Alkali a Jos. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: UGC

Mai shari’a Arum Ashom ne ya dage zaman zuwa ranakun 28 da 29 ga watan Mayun 2025 domin ba masu kare kai damar gabatar da shaidunsu a kotu, cewar Aminiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe Janar Idris Alkali a Jos

Janar Alkali ya ɓace ne a 2018 yayin da yake tafiya daga Abuja zuwa Bauchi ta Jihar Plateau a lokacin da ya riga ya yi ritaya.

Janar Mohammed, wanda shi ne kwamandan Runduna ta 3 a wancan lokaci ya jagoranci aikin neman Alkali bayan ɓatarsa.

Shi ne ya jagoranci aikin gano motar mamacin a cikin wani rami mai zurfi a yankin Du da ke Jihar Plateau.

Daga bisani kuma aka gano gawar tsohon Janar ɗin a cikin tsohuwar rijiya a kauyen Guchwet a gundumar Shen.

Dalilan kotu na dage shari'ar da ake yi kan kisan Janar Alkali
Kotu ta dage shari'ar kisan gilla kan Janar Alkali zuwa watan Mayu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Depositphotos

Janar Alkali: Matakin da kotu ta ɗauka?

Wannan na zuwa ne bayan bangaren masu ƙara sun kammala tambayar Manjo-Janar U.I Mohammed wanda ya ba da shaida kan binciken kisan.

Kara karanta wannan

'Masarauta ta girmi haka': Shehu Sani kan gayyatar Sarki Sanusi II, ya nemo mafita

A zaman kotun na ranar Litinin, lauyan masu kare kai ya tambayi Janar Mohammed domin ƙarin bayani kan shaidunsa.

Tambayoyin sun shafi bayanan da ya bayar tun farko da kuma abin da ya bayyana a lokacin da ya fara ba da shaida.

Bayan kusan awanni biyu ana tambayoyi, kotu ta sallami shaidar tare da ɗage zaman zuwa wani lokaci.

Lauyan gwamnati, Simon Mom, wanda ya wakilci Babban Lauyan Jihar Plateau, bai nuna adawa da dagewar ba.

Daga karshe, Mai shari’a Arum Ashom ya sanar da cewa za a ci gaba da sauraron karar a ranakun 28 da 29 ga watan Mayun 2025.

An kama wani kan zargin kisan Janar Alkali

Mun ba ku labari a baya cewa Rundunar yan sandan Najeriya ta sanar da kama wani mai laifi daga cikin wadanda ake zargi da hannu cikin kisan Manjo -Janar Idris Alkali.

Marigayin shi ne tsohon shugaban sha’anin mulki a hedikwatar rundunar Sojan kasa, wanda aka hallaka a Jos na jihar Plateau.

Rahotanni sun ce an cafke ‘kanwa uwar gami’ a harin ne bayan daukan tsawon lokaci ana bin sawunsa sakamakon cika wandonsa da iska da yayi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng