Karshen Wahala: Janar Tsiga Ya Sami Ƴanci bayan Watanni 2 a Hannun Ƴan Bindiga

Karshen Wahala: Janar Tsiga Ya Sami Ƴanci bayan Watanni 2 a Hannun Ƴan Bindiga

  • Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ya kubuta bayan shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa da mutane a jihar Katsina
  • Legit.ng ta rahoto cewa an sace Tsiga da wasu a ranar 5 ga Fabrairu, 2025, kuma an ci gaba da tsare shi duk da an biya kuɗin fansarsa
  • Wasu sun ce an biya 'yan bindigar N60m, amma wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa adadin da aka biya ya nunka hakan sau uku
  • To sai dai an tabbatar da cewa 'yan bindigar sun saki Janar Tsiga ba tare da an ƙara masu kuɗi ba, kuma yanzu yana kan hanyar Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ya samu ‘yanci bayan shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa da mutane.

Legit.ng Hausa ta ruwaito yadda tsohon Darakta-Janar na NYSC ya faɗa hannun masu garkuwa da mutane a garinsu na Bakori, da ke jihar Katsina.

Kara karanta wannan

'Mun sha azaba': Janar Tsiga ya magantu, ya fadi dabbobin da suke kwana tare da su

Majiyoyi sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun saki Janar Maharazu Tsiga bayan kwanaki 56 a tsare
Katsina: 'Yan bindiga sun saki Janar Maharazu Tsiga bayan kwanaki 56 a tsare. Hoto: Abdullahi Tsiga
Asali: Facebook

Yadda aka sace da tsare Janar Maharazu Tsiga

An sace Janar Tsiga tare da wasu mazauna garin su tara a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa, amma rahoton ya nuna cewa masu garkuwar sun ci gaba da tsare shi na tsawon makonni.

Bayanan da aka samu kan biyan kuɗin fansar sun bambanta tsakanin majiyoyi mabanbanta da aka tattauna da su game da lamarin.

An tsare Janar Tsiga duk da biyan kudin fansa

Wasu sun ce Naira miliyan 60 aka biya, amma rahotanni masu ƙarfi sun shaida cewa adadin da aka biya ya nunka hakan sau uku.

Wani daga cikin iyalansa, ya shaida wa manema labarai cewa bayan an miƙa musu kuɗin, masu garkuwar sun daina tuntubar iyalan Tsiga na tsawon sati guda.

"An kai musu kuɗin, amma sai bayan mako guda, watau a ranar Talata, 11 ga Maris, suka kira waya kuma muka ji muryarsa," inji majiyar.

Kara karanta wannan

Janar Tsiga: An ji yadda tsohon shugaban NYSC ya kubuta daga hannun 'yan bindiga

An sako Janar Tsiga bayan kwanaki 56

Iyalan Janar Tsiga sun fadi inda ya ke bayan 'yan bindiga sun sako shi
'Yan bindiga sun sako Janar Tsiga bayan kwanaki 56, an tafi da shi zuwa Abuja. Hoto: Abdullahi Tsiga
Asali: Facebook

Majiyar ta ƙara da cewa masu garkuwar sun sake kira ne a lokacin domin neman ƙarin kuɗi, amma ya ce ba a ƙara masu ko sisin kwabo ba.

Majiyar ta kara da cewa:

“Ba a ƙara musu ko sisin kwabo ba, kuma yanzu haka da na ke magana da kai suna Zamfara, daga nan za su kai Janar din Abuja."

Wani babban jami’in soja ma ya tabbatar wa jaridar cewa 'yan bindiga sun saki Janar Tsiga, sannan majiyoyi daga danginsa sun tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya.

'Yan bindiga sun nemi N250m kan Tsiga

Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan bindigar da suka sace tsohon shugaban NYSC, Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), sun kira iyalansa ta waya don neman kudin fansa.

Masu garkuwar sun bukaci iyalan su biya su Naira miliyan 250 a matsayin kuɗin fansa kafin su sako Janar Tsiga.

Wani mazaunin garin Tsiga ya ce ana ta yaɗa bayanan adadin kuɗin da aka nema, amma iyalan na ƙoƙarin ɓoye lamarin saboda dalilan tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng