'Yan Bindiga Sun Sace babban Malamin Addini a Imo, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki
- An sace Rev. Fr. John Ubaechu, faston Cocin Holy Family Catholic da ke Izombe, a kan hanyarsa ta zuwa taron shekara na fastoci
- Kakakin Archdiocese na Owerri, Rev. Fr. Patrick Mbarah, ya bukaci Kiristoci da su dage da addu’a don ganin malamin ya kubuta cikin aminci
- Rundunar ’yan sandan Imo ta fara aikin leƙen asiri don gano inda aka boye faston tare da ceto shi, sannan ta nemi hadin kan jama’ar jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Imo - ’Yan bindiga sun sace faston Cocin Katolika, Rev. Fr. John Ubaechu, a Ejemekwuru, yankin karamar hukumar Oguta da ke jihar Imo.
Kakakin kungiyar Archdiocese na Owerri, Rev. Fr. Patrick Mbarah, ya tabbatar da sace faston a wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Twitter
'Yan bindiga sun sace malamin addini a Imo

Kara karanta wannan
"Ba ni da hannu," Sheikh Sulaimon ya fashe da kuka a tafsirin Ramadan, ya rantse da Alƙur'ani
A cewarsa, an sace Ubaechu, fasto a Cocin Holy Family Catholic da ke Izombe, a kan hanyarsa ta zuwa taron shekara na fastoci, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a kan titin Ejemekwuru da ke Oguta, inda aka bukaci jama'a da su sanya malamin a addu’o'insu.
Rev. Fr. Patrick Mbarah ya ce yanzu lokaci ne na neman taimakon Uwar Yesu mai tsarki domin ta kawo dauki don ganin malamin ya kubuta.
"Mun fawwala lamarin ga Uwar Yesu" - Mbarah
Sanarwar ta ce:
“Muna neman addu'ar mutane kan halin da muke ciki. 'Yan bindiga sun sace Rev. Fr. John Ubaechu da yammacin Lahadi, 23 ga Maris, 2025.
“Rev. Fr. Ubaechu shi ne faston Cocin Holy Family Catholic da ke Izombe. An sace shi ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa taron shekara na fastoci.
“Muna neman daukacin mabiya addinin Kirista da masu kyakkyawar niyya su yi addu’a don Ubangiji ya kubutar da shi cikin gaggawa.
"Mun fawwala lamarin Rev Fr John Ubaechu ga Uwar Yesu, Uwargidan fastoci, domin ganin ya samu kubuta daga 'yan bindigar cikin aminci."
'Yan sanda sun fadi matakin da suka dauka

Asali: Original
The Guardian ta rahoto cewa, rundunar ’yan sandan jihar Imo ta tabbatar da sace faston, inda ta bayyana cewa an sace shi ne a kan titin Ejemekwuru da ke Oguta.
Kakakin rundunar, Henry Okoye, ya ce an kaddamar da bincike domin gano wadanda ke da hannu a sace malamin addinin Kiristan.
Henry Okoye ya ce:
“Rundunar ’yan sandan Imo ta kaddamar da bincike domin cafke wadanda suka sace Rev. Fr. John Ubaechu a ranar Lahadi, 23 ga Maris, 2025.”
“Ana gudanar da aikin leƙen asiri da nufin kubutar da faston, yayin da rundunar take bukatar hadin kan jama’a don samar da bayanan da za su taimaka wajen gano inda aka boye shi.”
An bukaci jama’a da su tuntubi ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kira layukan gaggawa 08034773600 ko 08158024755 don bayar da bayanai.
'Yan bindiga sun harbi malamin addini a Delta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai hari kan wani coci a Delta, inda suka harbi fasto tare da sace mutum shida, ciki har da masu gadi biyu.
Matar faston ta ce maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya jikkata mijinta, inda harsashi ya samu kafarsa har ya rasa yatsunsa biyu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng