Ramadan: Dan Majalisa Kirista Ya Yi Wa Musulmi Bazata bayan Bukatar Babban Limami
- Dan majalisar tarayya na mazabar Ogbaru, Hon. Victor Afam Ogene, ya sha alwashin gina babban masallaci ga al’ummar Musulmi a yankin
- Ogene ya bayyana hakan ne lokacin da ya halarci bude baki tare da Musulmi a lokacin azumin Ramadan da ake ciki
- Ya ce duk dan Najeriya na da ‘yancin zama a kowane yanki kuma ba ya fifita addini ko wani bangare a kan wani
- Limamin Musulmi ya yaba da halartar Ogene, ya kuma ce za su ci gaba da yi masa addu’a da goyon baya a siyasarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ogbaru, Anambra - A cikin yanayin zaman lafiya, dan majalisar Ogbaru a jihar Anambra, Hon. Victor Afam Ogene, ya yi alkawarin gina babban masallaci.
Hon. Ogene dan jam’iyyar LP ne a majalisa kuma shugaban kwamitin makamashi, ya yi wannan alkawari a lokacin bude baki.

Asali: Facebook
Bukatar da liman ya nema wurin dan majalisa
Yayin amsa roƙon Liman Abdul Majeed Oniyan, Ogene ya tabbatar da cewa Musulmi za su samu rabon dimokuraɗiyya kamar sauran al’umma, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan majalisar ya ce akwai kyakkyawar alaka tsakanin Musulmi a yankin da sauran al'umma saboda shekarun da suka shafe a wurin.
Ya ce:
“Da dama daga cikinku kuna zaune a Ogbaru shekaru da dama; kuna haihuwa da kasuwanci anan, kuma kundin tsarin mulki ya yarda da haka.”
“Ina mai tabbatar muku, ba na fifita addini, kun nemi masallaci, in Allah ya raya mu zuwa badi, zan taimaka ku samu.”

Asali: Original
Rokon da dan majalisar ya yi ga Musulmi
Hon. Ogene ya roƙi Musulmi su yi amfani da lokacin azumi wajen yin addu’a domin zaman lafiya da ci gaba a Najeriya baki ɗaya.
A baya, Liman Oniyan ya yaba wa Ogene da kasancewa dan majalisa na farko da ya zo ya bude baki tare da su, Punch ta ruwaito.
Ya ce wannan ziyara ta karfafa dangantaka, kuma za su ci gaba da yi masa addu’a da maraba da shi a masallaci.
Ya kara da cewa:
“Za ka iya zama shugaban Najeriya, muna yi maka addu’a, kuma nasararka alamar zabin Allah ce, muna tare da kai gaba daya.”
“Yau 21 ga watan Ramadan ne, muna amfani da Alkur’ani wajen yi maka addu’a da goyon baya a harkokin siyasa.”
A lokacin ziyarar, Hon. Ogene ya kuma raba kayan abinci da kuɗi ga Musulmin yankin a matsayin taimako musamman saboda halin da ake ciki ga kuma Ramadan.
Legit Hausa ta yi magana da wani a Imo
Wani Musulmi da ke Okigwe a jihar Imo ya yabawa dan majalisar kan abin alheri da ya yi.
Usman Umar ya ce a gaskiya suna da kyakkyawar alaka tsakaninsu da ƴan siyasa a yankin musamman a wannan lokaci.
"Suna yi mana kokari musamman a irin wannan lokuta da kuma daukar nauyin wasu zuwa aikin hajji."
- Cewar Umar
Umar ya bukaci hadin kai tsakanin Musulmi da ke rayuwa a can da al'ummar yankunan.
Gwamna Nwifuru ya bukaci daukar nauyin mahajjata
Kun ji cewa Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya bukaci shugabannin kananan hukumomi 13 su dauki nauyin akalla Mahajjaci daya don aikin Hajjin 2025.
Majalisar zartarwa ta jihar ta amince da kashe N500m domin daukar nauyin Mahajjata 46, yayin da kowane shugaban karamar hukuma zai dauki guda daya.
Sai dai wasu mazauna jihar sun yi tir da matakin, suna mai cewa ana da sauran matsaloli kamar yajin aikin malaman firamare da ya kamata a warware.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng