Zo Ka Nema: Gwamna Fintiri Zai Horar da Matasa, Akwai Tukuicin N10,000 duk Wata
- Gwamna Ahmadu Fintiri ya ƙaddamar da shirin koyon sana’o’i domin bai wa matasa da mata horo a fannoni daban-daban na rayuwar
- Gwamnatin jihar ta farfaɗo da cibiyoyin koyon sana’o’i guda 10 tare da samar da kayan aikin zamani domin ba da horo mai inganci
- An zaɓi sana’o’in ne bisa bukatun kasuwar aiki, don bai wa mahalarta damar samun aiki ko kafa nasu kasuwancin a Adamawa da fadin kasar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Adamawa - Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ƙaddamar da shirin koyon sana’o’i domin taimaka wa matasa da mata su samu horo a fannoni daban-daban.
Sanarwar da aka fitar a ranar Asabar, 22 ga watan Maris, ta bayyana cewa Gwamna Ahmadu Fintiri ya aiwatar da shirin ne ta hannun hukumar rage talauci da kirƙirar hanyar samun arziki (PAWECA).

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shirin zai haɓaka ƙwarewar jama’a kan sana'o'i, inganta iliminsu, da samar da damarmakin bunkasa tattalin arziki a faɗin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fintiri ya farfaɗo da cibiyoyin koyon sana’o’i
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa Gwamna Fintiri na da ƙudurin rage rashin aikin yi da kuma ƙarfafa dogaro da kai ga matasa da matan Adamawa.
Don haka, an farfaɗo da cibiyoyin koyon sana’o’i guda 10, inda aka sanya masu kayan aiki na zamani domin ba da ingantaccen horo ga mahalarta shirin.
Rahoton Legit.ng ya nuna cewa waɗannan cibiyoyi za su zama tushen koyar da sana’o’i da dabarun fasaha, ta yadda masu cin gajiyar shirin za su samu ƙwarewa a fannonin da suke da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki.
Jerin sana'o'in da za a koyar
Sanarwar ta bayyana cewa shirin zai ba da horo a fannonin fasaha da sana’o’i daban-daban, waɗanda suka haɗa da:
- Fasahar kanikanci
- Hada wutar lantarki da gyarawa
- Walda da sarrafa karfe
- Gyaran wayoyin salula
- Gyaran mota
- Sanya tayils da POP
- Fasahar dinki da ado
- Hada nau'o'rin hasken rana zuwa wutar lantarki
- Kafitanci da sarrafa katako
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an zabi fannoni ne domin sun dace da bukatun kasuwar aiki na yanzu, kuma samun ilimi kan su zai bai wa mahalarta shirin damar samun aiki ko kafa nasu kasuwancin a jihar ko sassan kasar baki daya.
Gwamnati ta yi alkawarin ba da tukuici
Domin bai wa mutane masu yawa damar amfana da shirin, an tsara ba da horon a wa’adi uku:
- Gajeren horo (watanni 3)
- Matsakaicin horo (watanni 6)
- Babban horo (shekara 1)
Bugu da ƙari, gwamnatin jihar ta sanar da shirin ba wa kowane ɗalibi da ke halartar horo tallafin N10,000 a kowane wata domin rage musu matsin tattalin arziki.
A cewar sanarwar, gwamnati ba ta shirya shirin don ba da horo kadai ba, har ma da saka hannun jari ga makomar jihar Adamawa.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Sabuwar barazana ta tunkaro Sanata Natasha kan zamanta a majalisa
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“Yayin da duniya ke mai da hankali kan ilimin sana’a da koyon fasahohi na zamani a matsayin ginshiƙan bunƙasa tattalin arziki, Adamawa ta ɗauki matakin jagoranci a fannin ƙarfafa sana’o’i, samar da ayyukan yi da rage fatara.”
Fintiri ya gargadi jami'an gwamnati kan siyasa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga masu rike da muƙamai a gwamnatinsa.
Gwamna Fintiri ya gargaɗi mutanen da ya ba muƙamai da su ajiye burinsu na siyasa a 2025 su maida hankali wajen gina jihar.
Asali: Legit.ng