Jerin kasashe biyar a duniya da suke da saukin samun aiki

Jerin kasashe biyar a duniya da suke da saukin samun aiki

- Najeriya bata shiga cikin jerin kasashe 5 da aiki ke saukin samuwa ba, a cikin jerin da aka yi na kasheshi 127

- Najeriya ta shiga cikin kasashe 5 na can kasa tare da kasashen da yaki ya cinye irinsu Libiya da Syria

- Yayin da Turai da Jamus suka zama na can sama, Amurka ta zo a ta hudu, Japan kuwa tazo ta biyar cikin jerin

Wani tsari na jera kasashen da suke da saukin samun ayyuka na shekarar 2020 ya fita, inda kasashe 5 na farko suka bayyana.

Cikin kasashe 5 na sama kuwa Ingila ce kasar farko a jerin, yayin da Jamus ta biyu, Canada kuwa ta samu fitowa a ta uku.

Amurka tazo a ta hudu, Japan tazo a ta biyar.

A dayan bangaren kuwa, Najeriya tana can kasan jerin tare da Yemen, Syria da Libya.

Wani shafi na Twitter mai suna Nairalytics, ya wallafa jerin kasashen bayan tsananin bincike da nazari akan kasashen guda 127.

Sunyi dubi ne akan abubuwa guda biyu, saukin rayuwa da kuma damar samun ayyuka.

Sakamakon wannan nazarin, sun fitar da jerin kasashen kamar haka:

Kasashe 5 na farko a jerin sune, Turai da tazo ta daya, Jamus ta biyu, Canada ta uku, Amurka a ta hudu sai Japan a matsayin ta biyar a jerin.

Kasashe 5 dake can kasa kuwa Uruguay ce ta 124, Najeriya ta 125, Libiya ta 126 sai Syria ta 127.

KU KARANTA: Yadda 'yan kungiyar asiri suka makantar da ni saboda na ki shiga kungiyarsu - Matashi

Jerin kasashe biyar a duniya da suke da saukin samun aiki
Jerin kasashe biyar a duniya da suke da saukin samun aiki.
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Borno: An rasa rayuka 3 a sabon harin 'yan ta'addan Boko Haram

Daga sakin jerin kasashen, nan da nan mutane suka fara cece-kuce akan matsayin Najeriya a jerin.

A wani labari na daban, a kowacce jiha a Najeriya, ba'a rasa masallatai masu kyau. Musulumci yana daya daga cikin manyan addinai da mutanen Najeriya har da Afirika sukayi imani da shi.

Musulunci ba addini kadai ya shafa ba, hatta gine-ginen Afirika ya shafa. Ana samun Masallatai masu kyau a kowacce jiha a kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel