FG za ta bawa matasa 500,000 horon koyon sana'o'in zamani

FG za ta bawa matasa 500,000 horon koyon sana'o'in zamani

- Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin bawa matasa horo a kan koyon sana'o'i ta hanyar sarrafa fasahar zamani

- Hakan na zuwa ne bayan FG ta sanar da fara biyan tallafin N30,000 ga masu sana'ar hannu 300,000 a rukunin farko na shirin bayar da tallafin

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta amince da ware makudan kuɗaɗe domin horar da matasa dubu ɗari biyar 500,000 sabbin sana'o'i ta hanyoyin sarrafa fasahar zamani.

Ministan harkokin matasa da wasanni, Sunday Dare, ne ya bayyana hakan a wani taron matasa da kamfanin NBC (Nigeria Bottling Company) ya ɗauki nauyi.

An kaddamar da shirin NBL (Nigeria Business League) domin taimakawa matasa su cimma burinsu na rayuwa gami da tunkarar ƙalubalen da ke gabansu.

Dare ya ce shirin bawa matasan horo yana karkashin tsarin tayar da komadar tattalin arziki na gwamnatin tarayya.

KARANTA: Gwamnati ta lissafa muhimman wurare 22 da mabarnata matasa suka lalata

A cewar Dare, za a shafe tsawon watanni 12 ana bawa matasan Najeriya horo.

A ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa gwamnatin tarayya ta sanar da kaddamar da shirin bunkasa tattalin arziki.

A karkashin wannan shiri, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta fara biyan N30,000 ga masu sana'ar hannu.

FG za ta bawa matasa 500,000 horon koyon sana'o'in zamani
Sunday Dare @legit.ng
Asali: Twitter

A cewar gwamnatin tarayya, za ta biya kudin sau daya ga kowanne mutum.

Kudin da aka fara rabawa na daga cikin kudaden da aka ware domin farfado da kananan masana'antu da bullar annobar korona ta kassara.

An fara biyan kudaden ne kai tsaye zuwa asusun masu sana'ar hannu da aka tantance a jihohi goma.

KARANTA: Sabon hari a Katsina: Yan bindiga sun sace mata uku yayin artabu da 'yan sanda, sun kashe Rabe Bala

Jihohi 10 da aka zaba a matsayin rukuni na farko tare da fara biyan mutanensu sun hada da; Abuja, Lagos, Kaduna, Ondo, Kano, Borno, Abia, Bauchi, Anambra, Ribas, Filato, da Delta.

Mutanen da aka zaba daga jihohin sun aika bayanansu ne a tsakanin 1 ga watan Oktoba zuwa ranar 10 ga watan Oktoba ta shafin yanar gizo da aka bude domin neman tallafin.

Shugaba Buhari ne ya kaddamar da shirin bawa kananan masana'antu tallafi (MSMEs Survival Fund) a cikin watan Maris, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel