Saka hannun jari: Jerin sunayen jihohi 10 da suka fi arziƙi a Nigeria a 2020

Saka hannun jari: Jerin sunayen jihohi 10 da suka fi arziƙi a Nigeria a 2020

Wani rahoto da jaridar The Cable ta fitar ya nuna cewa Legas ta kasance yankin Najeriya mafi soyuwa ga masu saka hannun jari yayin da take kan gaba a jerin jihohin da suka fi jawo hankulan masu saka jari a shekarar 2020.

Har ila yau bisa rahoton jihar Lagas din ta zarce sauran jihohin kasar ciki harda Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Legit.ng ta lura cewa rahoton wanda ya ambaci Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) a matsayin tushensa, ya nuna cewa Legas, cibiyar kula da tattalin arzikin Najeriya, ta jawo dala biliyan 8.31 a hannun jari.

KU KARANTA KUMA: Ka tsaya a layinka, hadimin Buhari ga Fani-Kayode bayan ya karyata batun komawarsa APC

Saka hannun jari: Jerin sunayen jihohi 10 da suka fi arziƙi a Nigeria a 2020
Saka hannun jari: Jerin sunayen jihohi 10 da suka fi arziƙi a Nigeria a 2020 Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

Wannan ya wakilci kaso 85.7 na jimillar jarin da ya shigo kasar nan a shekara ta 2020

Kalli jerin jihohin a kasa:

1. Lagos - $ 8.31 biliyan

2. Abuja (FCT) - dala biliyan 1.27

3. Abia - $ 56.07 miliyan

4. Niger - $ 16.36 miliyan

5. Ogun - $ 13.39 miliyan

6. Anambra - $ 10.02 miliyan

7. Kaduna - $ 4.03 miliyan

8. Sakkwato - $ 2.50 miliyan

9. Kano - $ 2.38 miliyan

10. Akwa Ibom - $ 1.05 miliyan

KU KARANTA KUMA: ‘Yan Majalisa za su yi wa sababbin hafsoshin tsaron da Buhari ya nada tankade da rairaya

A wani labarin, Kungiyar yan kwadago TUC ta caccaki gwamnatin tarayya kan sabon shirin da take yi na kara farashin man fetur sakamakon karuwan farashin danyen mai zuwa $60 ga ganga a kasuwan duniya.

TUC ta bayyana cewa gwamnatin nan ba ta tausayin yan Najeriya gaba daya, The Nation ta ruwaito.

A jawabin da shugaban kungiyar, Kwanred Quadri Olaleye, ya saki, ya ce gwamnati na azarbabin fadawa Najeriya farashi zai tashi amma ba ta gaggawa wajen cika alkawuranta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng