Tinubu ko APC: Jigon PDP Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Wanda Wike Yake Yi Wa Aiki
- Babban ƙusa a jam'iyyar PDP a Kudancin Najeriya, Cif Dan Orbih, ya taɓo batun aikin da Nyesom Wike yake yi a gwamnatin APC
- Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasan ya bayyana cewa ko kaɗan ba laifi ba ne idan Wike ya yi aiki a ƙarƙashin Bola Tinubu
- Dan Orbih ya yi nuni da cewa Wike ya sanar da jam'iyyar PDP kafin ya amshi tayin da aka yi masa na yin aiki a gwamnatin APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa (yankin Kudu maso Kudu), Cif Dan Orbih, ya yi magana kan rawar da Nyesom Wike yake takawa a gwamnatin APC.
Dan Orbih ya bayyana cewa ministan na babban birnin tarayya Abuja, y ana aiki ne don ƴan Najeriya, ba don APC ba.

Asali: Twitter
Dan Orbih ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a birnin tarayya Abuja a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya nemi iznin PDP kafin zama minista
Jigon na jam'iyyar adawa ya bayyana cewa Nyesom Wike ya nemi izini daga ɓangarorin da suka dace a jam’iyyar, kuma PDP ta ba shi dama ya yi aiki a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ya ce bisa ga hakan, bai kamata a samu wata matsala ba don Wike yana yin aiki tare da gwamnatin APC, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
“Kuma zan iya tabbatar muku cewa babu wata takarda da ke nuna cewa muƙaddashin shugaban jam’iyya na ƙasa da mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa, ko wani ɓangare na jam’iyyar, sun rubuta masa cewa ka da ya shiga wannan gwamnati."
"Ya rubutawa shugabannin yankin Kudu maso Kudu. Mun yi taro a Port Harcourt kuma baki ɗaya mun yarda cewa wannan aiki ne na hidimtawa ƙasa, don haka muka ba shi goyon baya."
“Ya rubutawa reshen jam’iyyar a jiharsa, kuma amsar da ya samu ta kasance mai kyau, an ce ya karɓi naɗin a matsayin wani nauyi na yin hidima ga ƙasa."
“Ya rubutawa mazabarsa da reshen jam’iyyar a ƙaramar hukumarsa. Babu wani ɓangare na jam’iyyar da ya fito fili ya ce a’a, ka da ya karɓi wannan muƙami."
"Ya rubutawa gwamnonin PDP, kuma zan iya tabbatar muku cewa bayan taron farko da suka yi, wata tawaga daga cikinsu ta tafi Abuja don taya shi murna."
- Dan Orbih
Ya jaddada cewa jam’iyyu dole ne su kula da yadda suke tafiyar da ƴaƴansu.
Jigon PDP ya kare Wike kan aiki da Tinubu
"Yanzu dai na gaya muku cewa shiga gwamnatinsa ba matsala ba ce, sai dai ga waɗanda ke da wata manufa ta daban."
“Lokacin da aka ba shi damar yin aiki a wannan gwamnati, ya rubutawa dukkan muhimman ɓangarorin jam’iyya, yana sanar da su cewa shugaban ƙasa ya gayyace shi don ya yi aiki a gwamnatinsa."
“Kuma na san cewa ba da jimawa ba, mambobin kwamitin amintattu sun gana da shi a gidansa, kuma a tsawon wannan taron, babu wanda ya kawo wannan batu."
"Don haka, Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ba ya na aiki ba ne don APC, ya na aiki ne don gwamnatin tarayyar Najeriya."
- Dan Orbih
Wike ya gana da Aminu Ado Bayero
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gana da ministan babban birnin tarayya Abuja.
Sarkin na Kano ya yi tattaunawar sirri ne da ministan kafin halartar bikin yaye dalibai na jami'ar Calabar da ke jihar Cross Rivers.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng