'Yan Bindiga Sun Je har Gida, Sun Kashe Shugaban Miyetti Allah ana cikin Azumi
- 'Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah na Barkin Ladi, Muhammad Adamu, a gidansa bayan ya gama buda baki a ranar Laraba
- Kugniyar MACBAN ta bayyana cewa marigayin ya tsallake yunkurin kisa sau uku a baya, amma wannan karo 'yan bindigar suka kashe shi
- An bayyana kisan Muhammad Adamu a matsayin abin bakin ciki, kasancewar ya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya a yankin
- Miyetti Allah ta reshen Filato, ta bukaci hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka kashe shugabanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) reshen karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.
Rahotanni sun bayyana cewa, miyagun sun aika Muhammad Adamu lahira a harin da suka kai gidansa a daren ranar Laraba, 19 ga Maris din 2025.

Asali: Twitter
'Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah
Shugaban kungiyar MACBAN na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da kisan, inda ya ce an harbe marigayin a gidansa bayan kammala buda baki, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibrahim Babayo ya la’anci harin tare da kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka aikata kisan.
Shugaban matasan yankin, Alhaji Danjuma Ibrahim, ya ce an ajiye gawar marigayin a asibitin karamar hukumar Barkin Ladi, kuma za a binne shi a ranar Alhamis.
Sau 3 ana farmakar shugaban Miyetti Allah
Alhaji Danjuma ya ce marigayin ya tsallake yunkurin kisa sau uku a baya, amma wannan karo ‘yan bindigar sun samu nasarar kashe shi.
"Sun harbe shi sau da dama a jikinsa. Bayan sun tabbatar ya mutu, ‘yan bindigar suka tsere," a cewar Danjuma.
The Guardian ta rahoton shugaban na MACBAN ya kara da cewa:

Kara karanta wannan
Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno
"Jami’an tsaro, ciki har da ‘yan sanda da sojoji, sun kai daukin gaggawa domin muna tare da su a asibiti a lokacin da aka shigo da shi a gaggauce."
Illar kisan Shugaban Miyetti Allah ga Filato

Asali: Original
Ya bayyana kisan shugaban MACBAN a matsayin abin bakin ciki, ya na mai cewa marigayin ya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya a yankin.
"Ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Barkin Ladi. Rasuwarsa za ta bar babban tabo a gare mu, saboda rawar da ya taka wurin dorewar zaman lafiya."
- Alhaji Danjuma.
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP Alabo Alfred, bai amsa kiran da aka yi masa ba.
Kisan Muhammad Adamu na zuwa ne kasa da kwanaki 14 da aka kashe shugaban Miyetti Allah na jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina.
Mun kawo rahoton cewa miyagun ƴan bindigar sun harbe Alhaji Idris Abubakar Sakaina har lahira a ranar Asabar, 8 ga watan Maris din 2025.
Shugabannin Miyetti Allah 7 da aka kashe
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun yi ajalin akalla shugabannin kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) bakwai a sassa daban daban na Najeriya.
Na baya-bayan nan shi ne Alhaji Amadu Surajo, muƙaddashin shugaban MACBAN na Katsina, wanda aka kashe a gidansa da ke ƙauyen Mai Rana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng