‘Yan bindiga sun yi shigan Soji, sun sace shugaban kungiyar Makiyaya da karfi-da yaji
- Miyagun ‘Yan bindiga sun sace Shugaban kungiyar MACBAN na jihar Kogi
- Wadannan mutane sun yi shigar sojojin kasa, suka shiga gidan Wakili Damina
- Jami’an tsaro sun samu labarin wannan ta’adi da aka yi a makon da ya wuce
Rahotanni daga jaridar Vanguard sun tabbatar da cewa wasu miyagun ‘yan bindiga sun sake yin ta’adi a jihar Kogi.
‘Yan bindiga sun sace shugaban kungiyar Miyetti-Allah Cattle Breeders Association of Nigeria watau MACBAN na reshen jihar Kogi, Wakili Damina.
Kamar yadda mu ka samu rahoto daga wurare daban-dabam, sakataren kungiyar MACBAN na Kogi, Adamu Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
KU KARANTA: A koma wa Allah ya yi maganin matsalar tsaro - Gwamna
A ranar Talata, 4 ga watan Mayu, 2021, Alhaji Adamu Abubakar ya shaida wa manema labarai a garin Lokoja cewa an yi awon gaba da Wakili Damina.
Adamu Abubakar ya ce an sace shugaban kungiyarsu ta makiyayan ne a ranar Juma’a da ta wuce.
A cewar sakataren Miyetti-Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, ‘yan bindigan da su ka yi wannan danyen aiki sun yi shiga sojojin Najeriya ne.
Wadannan miyagun ‘yan bindiga sun shigo har cikin gidansa da karfin tsiya, su ka yi gaba da shugaban wannan kungiya wanda aka fi sani da MACBAN
KU KARANTA: An yi ram da wani Soja da tulin harsashi a tashar Borno
Tuni dai kungiyar MACBAN ta sanar da jami’an tsaro game da abin da ke faru wa, ta aika wa kwamishinan ‘yan sanda na Kogi wannan mummunan labari.
MACBAN ta sanar da CP Ede Ayuba ne ta hannun mai ba mai girma gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello shawara a kan harkokin shari’a, Jerry Omodara.
Da aka tuntubi Kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya tabbatar da samun wannan labari, amma ya ce ba za su iya yin komai ba saboda ba a sanar da DPO na yankin ba.
A jiya ne mu ka ji cewa za a iya samun cikas daga 'yan ta'addan Boko Haram wajen kafa makarantar horas da malamai da ake so a ayi a garin Gwoza.
Da ya ke gabatar da kudirinsa a gaban majalisa, Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya ce‘Yan ta’addan Boko Haram sun fara dawowa Borno, Yobe da Adamawa.
Asali: Legit.ng