An Hallaka Wani Ɗan Fulani Makiyayi Tare Da Shanu 52 a Wani Sabon Hari a Jihar Plateu

An Hallaka Wani Ɗan Fulani Makiyayi Tare Da Shanu 52 a Wani Sabon Hari a Jihar Plateu

- Wani ɗan fulani makiyayi ya rasa rayuwarsa a yayin da yake tsakar kiwon dabbobinsa a Ƙauyen Maiyanga jihar Plateau

- Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutumin sannan aka ɗaure gawarsa kuma aka jefata cikin rijiya

- Shanu 52 daga cikin shanun mutumin sun ɓata, amma daga baya aka gano gawarwakin su

An kashe wani ɗan fulani makiyayi a wani sabon hari da aka kai ƙauyen Maiyanga ƙaramar hukumar Bassa jihar Plateau, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Daga Ƙarshe, Mataimakin Shugaban Ƙasa Osinbajo Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takara a 2023

Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah MACBAN na jihar, Malam Nura Abdullahi, yace an kashe mutumin ranar Alhamis sannan aka jefa gawarsa a cikin rijiya.

An Hallaka Wani Ɗan Fulani Da Shanu 52 a Wani Sabon Hari a Jihar Plateu
An Hallaka Wani Ɗan Fulani Da Shanu 52 a Wani Sabon Hari a Jihar Plateu Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban MACBAN ɗin ya bayyana yadda lamarin yafaru da cewa:

"An farmaki Wani ɗan fulani mai suna Umar Muhammad Musa, ɗan shekara 40, yayin da yake kan hanyarsa ta kaiwa yayan sa dake kiwon dabbobi abinci, inda aka hallaka shi a wani ƙauye kusa da garin Kuru, ƙaramar hukumar Jos ta Kudu."

"An gano gawarsa ɗaure da duwatsu a cikin wata rijiya, wacce sai da aka saka injina uku suka kwashe ruwan dake cikinta kafin a sami damar fito da gawar."

"Shanun sa 52 sun ɓata, amma daga baya aka gano gawarwakin su a ƙauyen Maiyanga dake ƙaramar hukumar Bassa."

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Wani Tsohon Soja Dake Horad da Yan Ta'addan IPOB

Rahotanni sun bayyana cewa wakilin hukumar yan sandan yankin, wanda shine kwamandan runduna ta 6 'Operations Safe Haven,' Col. AH Gwani, ya halarci jana'izar mamacin.

Shugaban MACBAN na Barkin Ladi, Alhaji Shuaibu Bayaro, yayi kira ga hukumomin tsaro da suyi gaggawar ɗaukar matakin da ya dace a kan lamarin.

Yace: "Ina cigaba da lallashin matasan mu da suyi hakuri kada su ɗauki doka a hannun su. Ya kamata mu barwa jami'an tsaro da gwamnati suyi aikinsu, amma muna buƙatar ayi mana adalci."

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sanda, ASP Ubah Gabriel, yace zai gudanar da bincike kan lamarin kafin ya dawo ga manema labarai.

A wani labarin kuma Yajin Aiki: An Kulle Sakatariyar Gwamnatin Kaduna, Mambobin NLC Sun Mamaye Kan Hanyoyi

An kulle sakatariyar gwamnatin jihar Kaduna yayin da itama tashar jirgin ƙasa dake unguwar Rigasa take a kulle.

Mambobin ƙungiyar kwadugo sun cika titunan jihar Kaduna inda suke gudanar da zanga-zangar lumana kan matakin gwamnatin jihar na korar wasu ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262