A Ƙarshe, Majalisa Ta Ɗauki Matsaya kan Dokar Ta Ɓaci da Tinubu Ya Ayyana a Rivers

A Ƙarshe, Majalisa Ta Ɗauki Matsaya kan Dokar Ta Ɓaci da Tinubu Ya Ayyana a Rivers

  • Majalisar wakilai ta amince da bukatar shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers a zaman da aka yi a ranar Alhamis
  • ‘Yan majalisa 243 ne suka halarci zaman da ya amince da bukatar shugaba Tinubu, suka kada ƙuri’ar baki don amincewa da dokar
  • Majalisar ta kuma amince da dakatar da Gwamna Simi Fubara, mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin Rivers na watanni shida
  • Majalisar wakilai ta gyara dokar ta-ɓacin don bai wa shugaba Tinubu damar yin bitar dokar ko da bukatar hakan za ta taso a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa majalisar wakilai ta amince da bukatar shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Tinubu ya jawo wa kansa, dattawan Ribas sun faɗi matsayarsu kan dakatar da gwamna

A yayin zaman majalisar a ranar Alhamis, ‘yan majalisa sun amince da bukatar shugaba Tinubu ta hanyar ƙuri’ar baki.

Majalisar wakilai ta kada kuri'ar amince da bukatar Tinubu na ayyana dokar ta baci a Rivers
Majalisar wakilai ta amince da bukatar Tinubu na ayyana dokar ta baci a Rivers. Hoto: @HouseNGR, @officialABAT (X)
Asali: Twitter

Majalisa ta amince da bukatar shugaba Tinubu

Rahoton gidan talabijin na NTA ya nuna cewa 'yan majalisa 243 ne suka halarci zaman majalisar da ya amince da bukatar kafa dokar ta-baci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta kuma amince da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, da dukkan ‘yan majalisar jihar na watanni shida, kamar yadda Tinubu ya sanar.

Shugaban majalisar, Tajudeen Abbas, wanda ya jagoranci zaman, ya bukaci ‘yan majalisa su tofa albarkacin bakinsu yayin tattaunawa kan bukatar Shugaba Bola Tinubu.

Za a kafa kwamitin sulhunta rikicin Rivers

'Dan majalisa daga Benue, kuma mataimakin kakakin majalisar, Philip Agbese, ya bada shawarar kafa kwamitin sulhu domin sasanta rikicin siyasa a jihar Rivers.

Majalisar wakilai ta amince da shawarar kafa kwamitin sulhu domin daidaita matsala tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai ta ɗauki zafi kan buƙatar Tinubu na ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

Hakazalika, majalisar ta cimma matsayar cewa majalisar tarayya za ta karbi ragamar ayyukan majalisar dokokin Rivers na tsawon watanni shida.

'Ana jiran amincewar Sanatoci' - Onanuga

Majalisar ta kuma gyara ayyana dokar ta-ɓaci da aka ayyana a Rivers don bai wa shugaba Tinubu damar yin bitar dokar idan bukata ta taso.

A wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun Tinubu ya fitar a shafinsa na X, ya ce majalisar dattawa ma za ta yi zama kan wannan bukata a yau.

Kalli sanarwar Onanuga a nan:

Tinubu ya so gamuwa da matsala a majalisa

A hannu daya, mun rahoto cewa Tinubu na fuskantar matsala a majalisar dattawa dangane da dokar ta-ɓaci da ya ayyana a jihar Rivers.

Majiyoyi daga majalisar tarayya sun bayyana cewa magoya bayan Tinubu na fuskantar wahala wajen samun goyon bayan kaso biyu bisa uku da ake buƙata don amincewa da dokar.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Saboda rashin isassun ƙuri’u, majalisar dattawa ta ɗage muhawara kan batun zuwa Alhamis, yayin da wasu ‘yan majalisa ke kokwanto da matakin Tinubu.

Lauyoyi sun ga kuskuren ayyana dokar ta baci

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta soki dokar ta-ɓacin da shugaba Bola Tinubu ya ayyana a jihar Rivers.

NBA ta jaddada cewa sashe na 305 na kundin tsarin mulki bai ba shugaban ƙasa ikon dakatar da zababbun shugabanni da ‘yan majalisa ba.

Kungiyar ta bukaci a bi hanyoyin doka wajen warware rikicin siyasa, maimakon daukar matakai da ka iya yin barazana ga dimokuradiyya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng