EFCC Ta Cafke Akanta Janar, Ana Zargin Gwamnatin Bauchi Ta Wawure Naira Biliyan 70

EFCC Ta Cafke Akanta Janar, Ana Zargin Gwamnatin Bauchi Ta Wawure Naira Biliyan 70

  • Jami’an EFCC sun cafke Akanta Janar na Bauchi, Sirajo Jaja, tare da wasu mutane biyu bisa zargin karkatar da N70bn a madadin gwamnatin jihar
  • Ana zargin an cire Naira biliyan 59 daga asusun jihar, inda aka biya wakilan jam’iyya da abokan siyasar Gwamna Bala Mohammed da biliyoyin
  • Mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, wanda ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, ya kuma bayyana halin da ake ciki a yanzu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) sun cafke Akanta Janar na jihar Bauchi, Sirajo Jaja, bisa zargin badakalar N70bn.

An kama Sirajo Jaja a Abuja a ranar Laraba, 19 ga Maris, 2025, tare da Aliyu Abubakar na kamfanin Jasfad Resources Enterprise da wani mai sana'ar POS, Sunusi Ibrahim Sambo.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

EFCC ta magantu da ta cafke Akanta Janar na jihar Bauchi, da wasu mutane 2
EFCC ta kwamushe Akanta Janar na jihar Bauchi da wasu mutane 2 kan zargin wawure N70bn. Hoto: @SenBalaMohammed, @officialEFCC
Asali: Twitter

EFCC na binciken gwamnatin jihar Bauchi

Ana zargin wadanda aka kama da hannu a safarar kuɗi, karkatar da kudin jama’a da wawure Naira biliyan 70 a madadin gwamnatin jihar Bauchi, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta tabbatar da cewa binciken bai kyale Gwamna Bala Mohammed ba, domin shi ma ana kan bincikensa don gano ko da hannunsa a karkatar da kudin jihar Bauchi.

Rahotanni sun nuna cewa an cire Naira biliyan 59 daga asusun banki daban-daban, wanda shi Akanta Janar din ya bude a madadin gwamnatin Bauchi.

Ana zargin kudaden sun shiga hannun Aliyu Abubakar da Sunusi Sambo, waɗanda suka rarraba wa wakilan jam’iyya da abokan siyasar gwamnan.

An cafke Akanta Janar kan badakalar N70bn

Aliyu Abubakar, wanda ke gudanar da kasuwancin canjin kudi ba tare da lasisi ba, ya tsere wa hukumar bayan an ba da belinsa amma daga baya EFCC ta sake kama shi.

Kara karanta wannan

Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da kama wadanda ake zargi tare da bayyana cewa hukumar na cigaba da bincike.

Majiyoyin EFCC sun shaida wa jaridar Punch cewa wadanda aka kama sun taka rawa a safarar kudin da suka kai Naira biliyan 70.

"Ana zargin cewa kudin da aka cire daga asusun jihar an yi amfani da su wajen biyan wakilan jam’iyya da abokan siyasar Bala Mohammed."

- A cewar majiyoyin.

Ana binciken gwamna bayan haduwa da Obi

Bala Mohammed, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin PDP, yana daya daga cikin manyan masu sukar Gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

A makon da ya gabata, muka ruwaito cewa, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya kai wa Gwamna Bala ziyara a Bauchi.

A yayin ziyarar, Peter Obi da Bala Mohammed sun jaddada aniyarsu ta yin aiki tare domin kawar da gwamnatin Tinubu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya za ta raba tallafin kudin noma ga mutane 250,000

Hukumar EFCC ta ce yanzu haka tana ci gaba da bincike, kuma wadanda aka kama za su fuskanci hukunci idan an kammala binciken.

Wike zai kunna wuta a jihohin da ke hannun PDP

Tun da fari, mun ruwaiyo cewa, ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce zai kunno wuta a jihohin da jam'iyyar PDP ke mulki idan ba su guji tsoma baki a harkokin siyasar Ribas ba.

Da yake mayar da martani ga ƙungiyar gwamnonin PDP karkashin Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, Wike ya yi barazanar jefa rikici a jihohin da ke karkashin PDP a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng