Dakatar da Fubara: Da Gaske 'Yan Neja Delta Sun Kai Hari Matatar Fatakwal?
- Kamfanin man gwamnatin Najeriya na NNPCL ya ce labarin fashewar abubuwa a matatar mai ta Fatakwal ba gaskiya ba ne
- Mai magana da yawun NNPCL ya tabbatar da gobarar da ta tashi a wani bangare an kashe ta cikin gaggawa ba tare da wani lahani ba
- Biyo bayan karamar gobarar, NNPCL ya ce matatar na ci gaba da aiki kuma tana samar da kayayyakin mai kamar yadda aka saba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya tabbatar da cewa matatar mai ta Fatakwal na ci gaba da aiki duk da wata karamar gobara da ta tashi a wani bangare na matatar.
NNPCL ya yi bayani ne bayan rade radin da ake yadawa cewa an samu fashewar wasu abubuwa da aka ce an kai hari ne matatar.

Kara karanta wannan
Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci

Asali: UGC
Legit ta gano bayanin da kamfanin ya yi a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yammacin ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye, ya bayyana cewa labarin kai hari matatar ba gaskiya ba ne.
Yanayin siyasa a jihar Rivers
Sanarwar kamfanin NNPCL ta zo ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin siyasa a jihar Rivers, wanda ya kai ga dakatar gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.
A baya-bayan nan, gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-baci a jihar, lamarin da ya kara dagula al’amura.
Daga cikin dalilan da gwamnatin Bola Tinubu ta fada na saka dokar ta-baci akwai fasa bututun mai da aka yi a jihar bayan fara maganar tsige gwamna Fubara.
NNPCL ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa duk da wannan yanayi, matatar mai na aiki yadda ya kamata kuma babu wata barazana ga samar da kayayyakin mai.

Kara karanta wannan
Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno

Asali: Twitter
Babu abin fargaba a matatar Fatakwal - NNPCL
Kakakin NNPCL, Olufemi Soneye ya bayyana cewa bayan faruwar gobarar, an kashe ta cikin kankanin lokaci ba tare da wata matsala ba, kuma dukkanin sassan matatar na aiki.
"Kamfanin NNPCL na tabbatar wa da al'ummar Najeriya cewa babu wata matsala da za ta haddasa fargaba,
"domin dukkanin sassan matatar da aka gyara kwanan nan na aiki yadda ya kamata"
- Olufemi Soneye
Channels TV ya rahoto cewa ya kara da cewa matatar na ci gaba da samar da kayayyakin mai kamar yadda aka tsara, ba tare da wata tangarda ba.
Sake farfado da matatar Fatakwal
A watan Nuwamba na shekarar 2024, kamfanin NNPCL ya sanar da cewa matatar mai ta Fatakwal ta fara aiki bayan an shafe dogon lokaci ana gyaranta.
Gwamnatin tarayya ta zuba biliyoyin Nairori domin gyaran matatar da nufin rage karancin man fetur a kasar nan.
Fubara: 'Yan Neja Delta sun gargadi Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan Neja Delta sun gargadi shugaba Bola Tinubu kan matakin da ya dauka na dakatar da Simi Fubara a Rivers.
Shugabannin yankin sun ce suna jin tsaro kar lamarin ya jawo yakin sari ka noke da dawo fasa bututun mai a Neja Delta mai arzikin mai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng