"Ba ka Yi Mana Adalci ba," NLC Ta Yi Raddi ga Obasanjo kan Mafi Karancin Albashin N70,000
- Kungiyar Kwadago ta musanta zargin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo kan tilasta wa gwamnati biyan albashi mai kyau
- Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ya ce kalaman da Cif Obasanjo ya wallafa a cikin sabon littafinsa a kan NLC ba haka abin ya ke ba
- Ya dora alhakin gaza samun mafi karancin albashi mai kyau a kan sharuddan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gindaya masu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta musanta zargin da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi cewa sun gaza wajen cimma matsaya mai kyau kan mafi karancin albashi.
Duk da haka, NLC ta amince da cewa sabon mafi karancin albashi na N70,000 ba zai yi wa ma'aikatan Najeriya komai ba, ganin yadda ake fuskantar tsadar rayuwa a halin yanzu.

Kara karanta wannan
"An takura wa shugaban kasa" Seyi Tinubu ya kare mahaifinsa daga sukar 'yan adawa

Asali: Facebook
Arise News ta wallafa cewa, NLC ta dora alhakin ƙuntata wa ma’aikata kan Gwamnatin Tarayya da masu daukar ma’aikata da ke zaman kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NLC ta yi martani gaOlusegun Obasanjo
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa NLC ta mayar da martani kan suka da Obasanjo ya yi wa jagorancinta a cikin sabon littafinsa, inda ta ke ganin bai yi mata adalci ba.
A wata sanarwa da Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu, kungiyar ta musanta ikirarin Obasanjo cewa ma’aikata sun zama wanda ake cutar wa, maimakon a kare hakkinsu.
Ajaero ya bayyana cewa jagorancin ƙungiyar kwadago ya yi iya kokarinsa wajen cimma matsaya mai kyau duk da matsin lambar da gwamnatin tarayya ta yi wa tattaunawar.
"Muna da ra'ayi guda kan albashi," NLC
Shugaban NLC ya gamsu da yadda tsohon shugaba, Olusegun Obasanjo ya amince da kokensu na cewa rayuwa ta yi tsada matuka, saboda haka ma'aikata na bukatar karin albashi.
Ajaero ya ce:
"Muna farin cikin samun goyon bayan mutum irin tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo.
A cikin sabon littafinsa, Cif Olusegun Obasanjo ya maimaita hujjojinmu, inda ya ce: 'Mafi karancin albashi bai ma isa biyan kudin sufuri ba ga wasu ma’aikata, balle ciyarwa, haya da kula da iyali.’”
"Wannan ne dalilin da ya sa muka nemi N610,000 a matsayin mafi karancin albashi, wanda muka bayyana da cikakken bayaninsa.”
NLC ta fadi yadda ta cimma mafi karancin albashi
Ajaero ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta amince da biyan N250,000, wanda shi ne iyakar abin da ƙungiyar kwadago ta yarda da shi.

Asali: Facebook
Ya ce amma wannan tayi ya zo da sharudda da dama, kuma da an amince da su, zai kara ta'azzara matsalar matsin rayuwa ga ma'aikatan.
Shugaban ya ce kungiyar ta amince da karbar N70,000 domin zai fi sauki ga 'yan Najeriya, musamman idan aka duba karin litar fetur zuwa sama da N200 kowace lita da za a yi.

Kara karanta wannan
"Manufofinsa na amfanar kowa," Tanko Yakasai ya nemi Arewa ta mara wa Tinubu baya
NLC ta fadi alfanun mafi karancin albashi
Duk da haka, Ajaero ya ce akwai wasu ƙarin fa’idodi da aka haɗa da sabon mafi karancin albashi na N70,000, wadanda ma'aikata za su mora.
Fa'idojin da NLC ta lissafo sun hada da rage lokacin da ake ɗauka kafin a sake tattaunawa kan mafi karancin albashi daga shekaru biyar zuwa uku.
Sauran sun hada da samar da motocin CNG ga ma’aikata domin saukaka sufuri da kuma ba da kayan canza mota mai amfani da fetur zuwa CNG kyauta ga ma’aikata.
Zanga-zanga: Kungiyar NLC ta sauya shawara
A wani labarin, kun ji cewa wakilan kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) sun gana da jami’an gwamnati bayan an gudanar da zanga-zanga don nuna adawa da karin kudin kiran waya.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce an shirya wannan zanga-zanga ne domin tilastawa gwamnati janye karin, ko kuma a samar da mafita da zai rage radadin da ‘yan kasa ke fuskanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng