Bola Tinubu Ya Naɗa Fitaccen Malamin Addini na Sokoto, Kukah a Muƙami
- Fitaccen limamin cocin Katolika da ke jihar Sakkwato, Bishof Mathew Kukah ya samu muƙami a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Shugaba Tinubu ya naɗa Bishof Kukah a matsayin shugaban Majalisar Gudanarwa na jami'ar tarayya da ke Kachia a jihar Kaduna
- Tinubu ya naɗa shugabannin jami'ar da mambobin majalisar gudanarwa kuma ana sa ran makarantar za ta fara ɗaukar ɗalibai a 2025
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Bishof Matthew Hassan Kukah, babban malamin darikar Katolika a jihar Sokoto, a muƙamin gwamnati.
Shugaba Tinubu ya naɗa Bishof Kukah matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwa da na Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Kachia a jihar Kaduna.

Asali: Facebook
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya sanar da haka a wata sanarwa da aka wallafa a X ranar Litinin.

Kara karanta wannan
2027: Matasa sun kaucewa tafiyar El Rufai a SDP, sun kama Peter Obi da Gwamna Bala
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya naɗa shugabannin jami'a
Sanarwar ta bayyana cewa shugaba Tinubu ya kuma naɗa wasu manyan jami’an gudanarwa na jami’ar, da suka haɗa da:
- Farfesa Qurix Williams Barnabas a matsayin Shugaban Jami’a (Vice Chancellor),
- Sanusi Gambo Adamu a matsayin magatakarda a Jami’a
- Ibrahim Dalhat a matsayin Akawu (Bursar),
- Farfesa Daniel Abubakar a matsayin Babban Mai Kula da dakin karatu
Tinubu ya naɗa abokan aikin Kukah
Har ila yau, Shugaba Tinubu ya amince da naɗin mambobin majalisar gudanarwa na Jami'ar daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Waɗanda shugaban ya naɗa sun haɗa da Thomas Etuh (Arewa ta Tsakiya), Cif Fabian Nwaora (Kudu maso Gabas), Farfesa Femi Taiwo (Kudu maso Yamma) da Zarah Bukar (Arewa Maso Gabas).
Onanuga ya bayyana cewa an zaɓi duk waɗannan mutane ne bisa cancanta, ƙwarewa, da jajircewarsu wajen inganta harkar ilimi a Najeriya.
Tinubu ya buƙaci su yi aiki da kwarewa
Shugaban ƙasa ya bukaci sababbin shugabannin jami’ar da su jajirce wajen gina fubalin ci gaban makarantra, don ta zama cibiyar ƙwarewa da binciken ilimi
Tinubu ya roƙi waɗanda Allah ya ba shugabancin Jami'ar su ɗora ta a kan hanyar ci gaba daidai da shirin sabunta fata (Renewed Hope Agenda) na gwamnatinsa.
Bugu da ƙari, shugaba Tinubu ya yi kira ga sabbin shugabannin da su samar da tsare-tsaren ci gaba domin tabbatar da cewa jami’ar ta ɗauki ɗalibanta na farko a watan Satumba na 2025.
Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Kachia, wadda a baya aka sani da Jami'ar No, an canza sunanta ne bayan da gwamnatin tarayya ta karɓi ragamar mallakarta.
Bishof Mathew Kukah na daga cikin fitattun malaman addini a Najeriya da suka shahara wajen bayyana ra'ayoyinsu kan lamuran siyasa, zamantakewa da ci gaban al'umma.
Nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa a matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Kachia, yana nuna yadda gwamnati ke daraja gudunmawar da shugabannin addini za su iya bayarwa wajen ci gaban ilimi da kasa baki daya.

Kara karanta wannan
Mutuwa mai yankar ƙauna: Tsohon ɗan Majalisa ya rasu kwanaki 7 kafin bikin ƙarin shekara
A tsawon shekarun da suka gabata, Bishof Kukah ya kasance mai fadin albarkacin bakinsa game da yadda ake tafiyar da al'amuran kasa, yana sukar matsalolin da suka shafi shugabanci da rashin adalci.
Saboda haka ne ma wannan nadin da aka yi masa ya jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya.
Wasu na ganin cewa wannan wata dama ce da za ta bashi karin tasiri wajen taka rawar gani a bangaren ilimi, yayin da wasu kuma ke fargabar kada mukamin ya hana shi kasancewa murya mai karfi a cikin al'umma kamar yadda aka san shi a baya.
Shugaba Tinubu ya naɗa Jega a muƙami
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bai wa tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega muƙami a gwamnatinsa.
A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, ta ce Tinubu ya amince da naɗin Jega a matsayim mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin dabbobi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng