An Yi Ca kan NYSC bayan Barazana ga Mai Bautar Ƙasa da Ta Soki Gwamnatin Tinubu
- Wata ‘yar bautar kasa a Legas ta bayyana cewa tana fuskantar barazana daga jami’an NYSC bayan ta soki gwamnati a bidiyonta
- A cikin bidiyon, ta bayyana halin tsadar rayuwa, tana tambayar matakan da gwamnati ke dauka don saukaka wahalhalu
- Ta bayyana cewa tana samun sakonnin barazana, kuma jami’in NYSC ya kira ta yana umartarta da ta goge bidiyon da ta wallafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Wata ‘yar bautar kasa da ke jihar Legas ta bayyana cewa ta samu sakonnin barazana daga wasu bayan ta soki gwamnati.
Matashiyar ta ce hukumar NYSC na yi mata barazana bayan sukar gwamnatin Bola Tinubu kan tsadar rayuwa da ake ciki.

Asali: Twitter
NYSC: Bidiyo da ya jawo wa matashiyar matsala
Hakan ya biyo bayan wani bidiyo da @OneJoblessBoy ya wallafa a shafin X inda ta nuna bacin ranta kan halin tattalin arziki.

Kara karanta wannan
Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, ta bayyana yadda tattalin arzikin Najeriya ke tabarbarewa, tana nuna damuwa sosai.
Ta yi suka kai tsaye ga Shugaba Bola Tinubu, tana kiransa da "banzan shugaba" tare da tambayar abin da gwamnati ke yi don saukaka wahala.
Ta ce:
“Idan mutane da dama sun fara fadin abin da muke fuskanta, watakila gwamnati za ta fara sauyi. Ina magana ne ga shugaban kasa."
“Ina fitowa daga kasuwa inda na je sayen kayan abinci, sai na tarar da cewa farashin kaya ya kara hauhawa sosai."
“Duk mako farashin kaya na hauhawa, ina tambaya, mene ne gwamnati ke yi? Yaushe za a daina ganin hauhawar farashi?"
Matashiyar ta ce dukan kudadenta na karewa ne wurin sauran al'amuran rayuwa a bar maganar ajiye wa ko siyan wani abu mai amfani.
Ta kara cewa:
“Kowane kudi da nake samu na kashewa ne wajen biyan kudade, ko fita da abokai ma ba zai yiwu ba, kudin mota Uber N25,000 ne.
“Misali, Tinubu, kai mutum ne mara amfani. Me kake yi domin ceto tattalin arzikinmu? Wannan shi ne abin da muke tambaya."

Asali: Twitter
Wace barazana NYSC ta yi mata?
Bayan bidiyonta ya karade intanet, ta bayyana cewa ta fara samun sakonnin barazana da ake zargin daga jami’an NYSC ne.
Ta sake wallafa wani bidiyo inda wani jami’in NYSC ke kiranta, yana cewa:
“Kina da hankali kuwa? Ki goge bidiyon nan nan take.”
Ta sake wallafa wasu sakonni a inda ta ce:
“Ko na goge bidiyon ba zai canza komai ba, amma goge shi yana nufin idan sun hukunta ni, babu wanda zai sani.
“Me ya sa jami’an NYSC ke tambayar mutane su nuna ni? Ni ba wata ƴar fashi ba, na karanta dokokin NYSC, ban karya su ba."
“Ya ku NYSC, idan wani mai bautar ƙasa ya yi kuskure, me ya sa za ku tsoratar da shi haka? Wannan tsoro da kuke ba ni ya yi yawa."
“Kun ce in zo ofis ranar Litinin. Toh, zan zo. Amma me kuma? Me ya sa kuke bina kamar ni ba ‘yar kasa ba ce?”
Hukumar NYSC ba ta ce komai ba tukuna dangane da zarge-zargen da ta ke fadi a bidiyonta da kafafen sada zumunta.
Wani matashi mai bautar ƙasa ya zanta da Legit Hausa
Ibrahim Mohammed da ke bautar ƙasa a Kogi ya ce tabbas akwai littafi da ke dauke da dokokin hukumar kuma sun karanta.
A ɓangarensa ya ce dole mutum ya bi doka saboda a karkashinta kullum muke sobada daidaita rayuwarmu.
Ya ce:
"Ina tunanin fadin albarkacin baki daban da kuma irin wadannan kalamai masu tsauri ga shugabanni."
A ƙarshe, ya bukaci gwamnati ta yi kokarin samar da sauki ga al'umma domin gudun saba dokokin kasa.
An nada sabon shugaban hukumar NYSC
Kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Birgediya-Janar Kunle Nafiu a matsayin sabon Darakta-Janar na NYSC.
Birgediya-Janar Nafiu ya karbi ragamar shugabancin NYSC ne daga hannun tsohon Darakta-Janar, Birgediya Janar Yushau Ahmed.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng