Ana Batun Hadaka, Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Fargabar Tinubu kan 2027

Ana Batun Hadaka, Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Fargabar Tinubu kan 2027

  • Fadar shugaban ƙasa ta yi magana kan shirin da ƴan adawa suka fara yi na yin haɗaka kan zaɓen shekarar 2027
  • Hadimin Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa shugaban ƙasan ko kaɗan bai damu da batun zaɓe mai zuwa ba
  • Sunday Dare ya bayyana cewa abin da shugaban ƙasan ya sanya a gaba shi ne yadda zai inganta rayuwar ƴan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta yi magana kan abin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya a gaba.

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Bola Tinubu a halin yanzu ya mayar da hankali ne kan inganta rayuwar ƴan Najeriya, ba kan zaɓukan 2027 ba.

Tinubu ya yi magana kan 2027
Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu bai damu da zaben 2027 ba Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mahaddacin Kur'anin da suka sace a Katsina? An gano gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan adawa sun fara shirin haɗaka kan 2027

Ya ce babban nasarar da Shugaba Tinubu zai yi a ƙarshen wa’adinsa ita ce yadda zai iya kawo ci gaba ga tattalin arziƙin ƙasar nan.

Wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da aka fara buga kugen siyasa kan 2027 da fama da matsin tattalin arziki a ƙasar nan.

Manyan ƴan siyasa na ci gaba da ƙoƙarin kafa wata haɗaka da za ta iya ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027, inda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa SDP.

Me Bola Tinubu ya sanya a gaba?

"Shugaba Tinubu ba ya damuwa kan zaɓe mai zuwa. Abin da ke damunsa shi ne yadda zai kawo ci gaba ga ƴan Najeriya."
"Abin da ke damunsa shi ne yadda manufofin da ya aiwatar za su haifar da sakamako mai kyau."
"Yana damuwa ne da abin da zai faru da tattalin arziƙin ƙasar nan. Wannan ne burinsa."

Kara karanta wannan

"Mutane miliyan 1 za su samu": Ɗangote ya fara raba tallafin Naira biliyan 16 ga ƴan Najeriya

"Muna ganin yadda asusun ajiyar kuɗin ƙasashen waje ke ƙaruwa. Muna ganin yadda hauhawar farashin kaya ke raguwa. Muna ganin yadda ribar cinikayya ke ƙaruwa."
"Muna ganin yadda fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje ke ƙaruwa, yayin da shigo da su ke raguwa."
"Muna ganin hannun jarin da aka jawo na sama da dala biliyan 50. Muna ganin yadda farashin kaya ke raguwa."
"Muna da bayanai a bayyane, kuma muna da shugaban ƙasa da ke kan madafa, wanda ya tsaya kan ƙudurorinsa."
"Kuma ina ganin cewa a halin yanzu, ba zaɓukan da za a yi a gaba ba ne ke gabansa."
"A gare shi, abu mafi muhimmanci shi ne a ƙarshen wa’adinsa, ya iya cewa, 'Na inganta rayuwar ƴan Najeriya. Na sauya tattalin arziƙin ƙasar nan'."

- Sunday Dare

An yi wa shugaba Tinubu barazana

A wani labarin kuma, kun ji cewa rikicin siyasar da ke aukuwa a jihar Rivers, ya jawo an yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu barazana.

Kara karanta wannan

Al-Mustapha ya ziyarci Atiku awanni da sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP

Wata ƙungiyar ƴan ƙabilar Ijaw mai suna Supreme Egbesu Assembly (SEA) ta bayyana cewa idan aka tsige gwamna Siminalayi Fubara, za ta ba shugaba Tinubu mamaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel