'Yan Fashi Sun kai Hari Makaranta ana Suhur a Katsina, Sun Yi Kisan Kai

'Yan Fashi Sun kai Hari Makaranta ana Suhur a Katsina, Sun Yi Kisan Kai

  • 'Yan fashi sun kai farmaki makarantar sakandare ta gwamnati a Yashe, sun kashe mai gadi daya tare da jikkata wani
  • Maharan sun farmaki makarantan ne da asuba, sun yi wa masu gadin dukan tsiya kafin su tsere da na’urar wutar sola
  • Rahotanni sun nuna cewa an garzaya da wanda aka raunata asibitin Kankia don samun kulawar likitoci cikin gaggawa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Wasu ‘yan fashi da makami sun kai hari a makarantar sakandare ta gwamnati da ke Yashe, karamar hukumar Kusada a jihar Katsina.

A yayin da 'yan fashin suka kai harin, an ruwaito cewa sun kashe mai gadi daya tare da raunata wani.

Katsina
'Yan fashi sun kai hari makaranta a Kastina. Hoto: Legit
Asali: Original

Legit ta tattaro bayanai kan harin ne a cikin wani sako da mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa yan ta'adda bazata, sun hallaka rikakken ɗan bindiga a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun farmaki makarantar ne da asuba a lokacin suhur, inda suka sara masu gadi da adda kafin su tsere da wata na’urar wutar sola.

Harin ya sake jefa al’ummar yankin cikin fargabar rashin tsaro da ke addabar wasu sassan jihar Katsina.

Yadda aka kai hari a makarantar Katsina

Majiyoyi daga bangaren tsaro sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na asuba lokacin da ‘yan fashin suka dira makarantar.

Maharan sun far wa masu gadin makarantar da makamai, inda suka yi amfani da adda wajen farmakarsu.

Bayanai sun nuna cewa daya daga cikin masu gadin, Abdullahi Sanusi, mai shekaru 50, ya mutu nan take sakamakon munanan raunukan da ya samu.

Shi kuwa abokin aikinsa, Aliyu Ahmed, mai shekaru 65, ya jikkata matuka, wanda hakan ya sa aka garzaya da shi zuwa asibitin Kankia domin samun kulawar likitoci.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi tabargazar sace sarki da dare, an kama mutum 5

Yanayin tsaro a jihar Katsina

Jihar Katsina na daga cikin yankunan da ke fama da matsalolin ‘yan bindiga da ‘yan fashi da makami, lamarin da ke kara jefa al’umma cikin damuwa.

A kwanakin baya, hukumomi sun dauki matakan tsaurara tsaro a wasu yankuna, amma hare-haren na ci gaba da faruwa.

Wannan hari da aka kai makarantar sakandare na Yashe ya kara nuna bukatar kara tsaurara matakan tsaro a makarantu da wuraren taruwar jama’a.

Gwamnan Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda. Hoto: Ibrahim Kaullaha Muhammad
Asali: Facebook

Matakan da ake dauka a makarantar

Hukumar makarantar da hukumomin tsaro na jihar Katsina sun bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Jami’an ‘yan sanda sun sha alwashin kamo wadanda suka aikata wannan ta’asa tare da gurfanar da su gaban kuliya.

An bukaci gwamnati da ta dauki tsauraran matakai domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, musamman a makarantu da wuraren da yara ke karatu.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta zauna kan kudirin harajin Tinubu kafin amincewa da shi

An kama mutane 5 kan sace sarki

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Abuja ta bayyana cewa ta kama wasu mutane biyar da ake zargi suna da hannu wajen sace wani sarki.

'Yan bindiga sun shiga gidan sarkin ne cikin dare suka sace shi tare da wasu jikokinsa, daga nan kuma suka bi wasu gidaje suka kara sace mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel