Obasanjo Ya Hada Buhari da Tinubu, Ya Yi Musu Rubdugu a Sabon Littafinsa

Obasanjo Ya Hada Buhari da Tinubu, Ya Yi Musu Rubdugu a Sabon Littafinsa

  • Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya soki Muhammadu Buhari da Bola Tinubu kan cin hanci da rashawa
  • Obasanjo ya siffanta aikin titin Legas-Calabar da sabon gidan Mataimakin Shugaban Ƙasa a matsayin ɓata kuɗi
  • Gwamnatin tarayya ta mayar da martani, tana kare ayyukan, tana mai cewa su ne manyan tushen ci gaban ƙasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ita ce mafi muni wajen cin hanci da rashawa a tarihin Najeriya.

Ya kuma yi nuni da cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na bin wannan tafarki, ya yi zargin cewa watakila ta zarce ta Buhari wajen ɓata kuɗin jama’a.

Kara karanta wannan

Al-Mustapha ya ziyarci Atiku awanni da sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP

Obasanjo
Gwamnatin tarayya ta yi martani ga Obasanjo kan zargin rashawa. Hoto: Bayo Onanuga|Bashir Ahmad|Kola Sulaiman
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta maida martani, tana mai cewa ayyukan da Bola Tinubu ke yi suna da fa’ida mai yawa ga tattalin arzikin ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obasanjo: "An yi rashawa a lokacin Buhari"

Obasanjo ya bayyana a cikin sabon littafinsa, Nigeria: Past and Future, cewa gwamnatin Buhari ce ta fi kowace rashawa.

Tsohon shugaban kasar ya ce:

“Mafi munin ɓata kuɗin gwamnati da karfafa cin hanci sun faru ne a lokacin mulkin Muhammadu Buhari da karkashin Ministan Shari’a, Abubakar Malami.”

Tsohon Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ma na bin wannan hanya, inda ya ce:

“Bayan kusan shekaru biyu na mulkinsa, ana ci gaba da yaudara.”

Titin Legas-Calabar: Rashawa ko cigaba?

Obasanjo ya siffanta aikin titin Legas-Calabar da ake yi da kuɗi Naira tiriliyan 15.6 a matsayin ɓata kuɗi da rashin cancanta.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi aikin da ya yi da aka gaza lokacin Buhari, Jonathan, 'Yar'adua

Haka nan, ya yi suka ga kashe Naira biliyan 21 wajen gina sabon gidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, inda ya ce hakan ba komai ba ne illa hanyar ɓarna da cin hanci.

Obasanjo ya ce:

“Shugaba Tinubu ya kauda kai daga korafe-korafen da ake yi kan wannan aiki.
"Wannan kawai wata hanya ce ta yin ado da ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, alhali ‘yan ƙasa na cikin yunwa.”

Gwamnatin Tinubu ta mayar da martani

Fadar Shugaban Ƙasa ta maida martani mai zafi kan kalaman Obasanjo, tana mai kare aikin titin Legas-Calabar.

Mai taimaka wa shugaba Tinubu kan harkokin watsa labarai, Sunday Dare, ya ce:

“Wannan aiki babba ne da ke da fa’ida ga tattalin arzikin ƙasa.”

Shi ma Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa aikin ba na ɓarna ba ne, ya na da kima kuma ya na tafiya daidai.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace matashin da ya lashe gasar Kur'ani bayan ya gana da gwamna

Umahi
Ministan ayyukan Najeriya a wani taro. Hoto: David Umahi
Asali: Getty Images

Ya ce:

“Akwai masu sukar aikin, amma su na mantawa da fa’idarsa.
"Na karanta korafe-korafen da ke yawo a kafafen sada zumunta, amma ina tabbatar muku cewa an riga an kammala fiye da kashi 70% na aikin.”

Ministan ya ƙara da cewa za a kammala sashe na farko na aikin a shekara mai zuwa, yana mai cewa:

“Ina yaba wa Shugaban Ƙasa. Masu sukar sa suna jin haushin abin da ya ke yi, amma hakan ya na nuna cewa yana aiki.”

Bola Tinubu ya ce tattalin Najeriya na farfadowa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ce matakan da ya dauka na cire tallafin man ferur da sauransu suna kan hanya.

Tinubu ya ce shugabannin da suka gabata shekaru 50 da suka wuce sun gaza daukar matakan, wanda hakan ya kusa jefa Najeriya a babbar matsala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel