Sauƙi Ya Samu: Dangote Ya Ƙara Sauke Farashin Man Fetur daga N825

Sauƙi Ya Samu: Dangote Ya Ƙara Sauke Farashin Man Fetur daga N825

  • Matatar Dangote ta rage farashin man fetur daga N825 zuwa N815, wanda ya sa ‘yan kasuwa suka fara siyan mai kai tsaye daga matatar
  • Farashin shigo da fetur daga waje ya sauka zuwa N774.72 kan kowace lita, lamarin da ka iya rage farashin da ake sayarwa a gidajen mai
  • Dangote na fuskantar gasa daga man da ake shigo da shi daga waje, don haka matatar ta rage farashi domin ta ci gaba da riƙe kasuwarta a gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Ana ci gaba da ganin saukar farashin kai a Najeriya yayin da matatar man Dangote ta rage farashin fetur daga N825 zuwa N815 a ranar Alhamis.

‘Yan kasuwa sun amince da saukar farashin, inda suka fara siyan man kai tsaye daga Dangote maimakon daga hannun masu ajiyar man da ke zaman kansu.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci da fetur ya sauka a Najeriya': Minista ya zayyano alheran Tinubu

Matatar man Dangote ta sauke farashin fetur domin ci gaba da jagorantar kasuwar mai a kasar
Matatar man Dangote ta sauke farashin litar fetur zuwa N815. Hoto: Bloomberg
Asali: UGC

Faduwar farashin shigo da fetur ya shafi Dangote

Wannan ragin na N10 na iya tilasta wa masu rumbun ajiyar mai masu zaman kansu su rage farashinsu don su ci gaba da gogayya a kasuwar, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko a makon nan, rahotanni sun nuna cewa farashin shigo da mai daga ƙasashen waje ya sauka zuwa N774.72 kan kowace lita.

'Yan kasuwa sun yi hasashen cewa wannan ci gaba zai iya rage farashin da ake sayar da fetur a gidajen mai zuwa N800 kan kowace lita.

Farashin shigo da man na N774.72 ya haɗa da kuɗin jigila, haraji, da sauyin kuɗi, wanda ya sa ya fi tsohon farashin matatar Dangote rahusa da N50.28.

Saboda wannan bambancin farashi, yawancin ‘yan kasuwa suka fara fifita siyan man da aka shigo da shi daga ƙetare fiye da wanda matatar Dangote ke samarwa.

Dangote ya rage farashin litar man fetur

Kara karanta wannan

Sauki na tafe: 'Yan kasuwa za su iya sauke farashin fetur kasa da na Dangote

Kakakin kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ta Najeriya (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya ce idan farashin danyen mai ya ƙara sauka, zai iya janyo karin raguwar farashin fetur.

Domin kare kasuwarta, matatar Dangote, wacce ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana, ta rage farashin litar man fetur a ranar Alhamis.

Bayan ƙarin harajin N10 da hukumar NMDPRA ke karɓa, farashin man a rumbunan ajiyar mai ya sauka daga N830 zuwa N825 kan kowace lita.

Wani ɗan kasuwa da bai so a bayyana sunansa ba ya tabbatar da cewa ana sayar da litar man fetur tsakanin N826 zuwa N830 a wurare daban-daban.

IPMAN ta yi magana kan dalilin sauke farashi

Wani mai sayar da mai ya ce raguwar farashin na da nasaba da tsarin kasuwa, amma matatar ta janye wasu rasiɗin biyan kuɗi saboda kuskure a farashi.

Ƙungiyar IPMAN ta tabbatar da cewa matatar Dangote ta saukar da farashin ta ne domin ta iya yin takara da man da ake shigo da shi daga ƙetare, inji rahoton BusinessDay.

Kara karanta wannan

Kano: Fashewar tukunyar gas ta jawo asarar rai, ƴan sanda sun ɗauki matakin gaggawa

Ukadike ya bayyana cewa tsarin ‘yanci a kasuwa yana bai wa kowanne mai kaya damar daidaita farashi domin ya ci gaba da samun abokan ciniki.

Ya ƙara da cewa matatar Dangote tana da miliyoyin lita na fetur a hannunta, don haka ba za ta iya barin wasu su karɓe kasuwarta ba.

Yadda man fetur ya fara tsada a mulkin Tinubu

Idan baku manta ba, a shekarar 2023, lokacin bikin rantsar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da janye tallafin man fetur.

Tun wancan lokacin 'yan Najeriya ke sayen mai a sama da N500, wanda ya kuma jefa 'yan kasa cikin yanayin sayen kayayyaki a farashi mai tsada.

Tun bayan janye tallafin kayayyaki suka tashi da kusan kaso 100%, duk da cewa 'yan kasar ba su sami wata hanyar habaka kudaden shiga ba.

Har yanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago kan wannan karin farashi.

Kara karanta wannan

'Asara ne': Dillalan mai sun koka kan rage farashin fetur, sun kawo mafita mai ɗorewa

Inda za a samu feturin Dangote da araha

A wani labarin, mun ruwaito cewa, matatar Dangote ta bayyana sunayen gidajen mai da ke sayar da fetur ɗinta da araha a fadin Najeriya.

Alhaji Aliko Dangote ya fitar da wannan sanarwa ne don saukaka wa masu ababen hawa wajen gano inda za su samu man a farashi mai sauki bayan sauke farashin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan ta hanyar ba da tushen tashin farashin mai a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel