Zargin Lalata: Natsaha Ta Bude Sabuwar Baraka ga Akpabio a Kotu

Zargin Lalata: Natsaha Ta Bude Sabuwar Baraka ga Akpabio a Kotu

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta maka Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da wasu a kotu kan dakatar da ita
  • Rahotanni na nuni da cewa Sanatar ta ce dakatarwar sabawa umarnin kotu ne, inda take neman a tuhumi wadanda suka raina kotu
  • Bayanai da suka fito sun nuna cewa kotu ta gargadi Sanata Akpabio da wasu cewa saba wa umarnin kotu na iya jefa su cikin matsala
  • Hakan na zuwa ne da ake cigaba da samun takaddama tsakanin shugabancin Majalisa ta 10 da Sanatar kan zargi da ta yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bayan dakatarwar wata shida da Majalisar Dattawa ta yi mata, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta maka Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, a kotu.

Rahotanni da suka fito a sun tabbatar da cewa Sanata Natasha ta shigar da Akpabio kara ne kan zargin laifin raina umarnin kotu.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha ta kai karar Akpabio ga kungiyar 'yan majalisun duniya

Natasha
Natasha ta shigar da Akpabio kara kan zargin raina kotu. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Twitter

Vanguard ta wallafa cewa Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta ce dakatarwar ta sabawa hukuncin da kotu ta riga ta yanke a ranar 4 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan shigar da karar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, kotun ta yi gargadi kan yiwuwar hukunta Akpabio da wasu idan har suka ci gaba da bijirewa umarninta.

Sanata Natasha ta kalubalanci majalisa

A cikin takardar karar da ta shigar, Sanata Natasha ta bayyana cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio, tare da Sakataren Majalisa sun karya doka.

Punch ta wallafa cewa cikin wadanda ta shigar kara har da Shugaban Kwamitin Ladabtarwan Majalisa, Sanata Neda Imasuem, kan karya dokar kotu.

A cewar ta, kotu ta hana majalisar ci gaba da binciken da ta ke yi a kanta dangane da wani abu da ya faru a zaman majalisar a ranar 20 ga watan Fabrairu, amma duk da haka an dakatar da ita.

Kara karanta wannan

Akpabio ya kalubalanci hurumin kotu kan koken Sanata Natasha

Kotun, a wata sanarwa da ta fitar, ta gargadi wadanda ake karar cewa yin watsi da umarninta na iya sa a daure su a kurkuku.

An zargi majalisa da rashin girmama kotu

Sanarwar kotun ta bayyana cewa umarnin hana dakatarwar da aka bayar an mika wa Shugaban Majalisa da sauran wadanda ake karar a ranar 5 ga watan Maris.

Sai dai duk da hakan, an ci gaba da dakatar da Sanata Natasha, abin da kotu ta ce sabawa hukuncinta ne.

Har ila yau, kotun ta bai wa Sanata Natasha izinin wallafa takardar karar a ginin Majalisar Dokoki ko a jaridun kasa domin tabbatar da an isar da sakon ga wadanda take kara.

Me Akpabio ya ce kan umarnin kotun?

A nasa martanin, Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio, ya kalubalanci ikon kotu na yin katsalandan a harkokin majalisa.

A yanzu haka dai, kotun ta daga sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Maris, inda za a ci gaba da nazarin karar da Sanata Natasha ta shigar.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha: Shugaban Majalisa, Akpabio ya dira kan ƴan Najeriya

Shugaban majalisa
Shugaban majalisa, Sanata Akpabio. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Sanatocin da aka buga da su a majalisa

A wani rahoton, kun ji cewa tun fara majalisa ta 10 ake kai ruwa rana da wasu Sanatoci kan wasu abubuwan da suka faru.

Sanata Ali Ndume da Abdul Ningi na cikin wadanda aka buga da su a majalisar, sai kuma Sanata Natasha da ake takaddama da ita a yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel