'Yan Bindiga Sun Sace Matashin da Ya Lashe Gasar Kur'ani bayan Ya Gana da Gwamna
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun tare hanya sun yi awon gaba da wasu ƴan gida ɗaya a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina
- Ƴan bindigan sun sace wani matashi wanda ya lashe gasar karatun Kur'ani tare da ƴan uwansa lokacin da suke hanyar komawa gida
- Majiyoyi sun bayyana cewa tun bayan da aka sace su a ranar Talata, har ya zuwa yanzu ba a sake jin ɗuriyarsu dangin mahaddacin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun sace wani mahaddaci mai suna Abdulsalam Rabi’u Faskari, wanda ya zama gwarzon gasar karatun Alkur’ani mai girma, a jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun sace Abdulsalam ne tare da mahaifinsa Malam Rabe Faskari da ƴan uwansa a kusa da ƙauyen Labin Bangori a jihar Katsina.

Asali: Original
Ƴan bindiga sun sace mahaddacin Al-Kur'ani
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kai musu harin ne a yammacin ranar Talata, lokacin da suke dawowa daga garin Katsina zuwa Faskari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Suna dai komawa gida ne bayan da Gwamna Dikko Radda ya karrama Abdulsalam saboda nasararsa a gasar karatun Alkur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Birnin Kebbi, jihar Kebbi.
Wani jami’in gwamnati daga ƙaramar hukumar Faskari, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
"An sace Malam Rabe da ƴaƴansa biyar, ciki har da Abdulsalam a ƙauyen Bangori a kan titin Yankara. Har yanzu ba mu sake jin ɗuriyarsu ba."
- Wani jami'in gwamnati
Abdulsalam dai ɗalibi ne a fannin likitanci a kami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, kuma ya lashe gasar karatun Alkur’ani a ɓangaren maza na haddar hizifi 60.
Wannan babbar nasara da ya samu ta jawo masa yabo daga cikin gida da waje, musamman daga malamai da shugabanni masu kishin addini da ilmi.
Ƴan sanda ba su ce komai ba
Har zuwa yanzu, rundunar ƴan sandan Jihar Katsina ba ta bayar da wata sanarwa kan lamarin ba.
Kakakin ƴan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Ƴan bindiga sun addabi mutane da hare-hare
Satar mutane da ƴan bindiga ke yi a yankin Arewa maso Yamma, musamman a jihar Katsina, na ci gaba da haifar da damuwa a zukatan jama'a.
Mutane da dama sun kasance cikin fargaba sakamakon irin waɗannan hare-hare da ke faruwa a kan manyan hanyoyi da ƙauyuka.
Al’ummar yankin da abin ya shafa suna ci gaba da addu’o'i tare da fatan kuɓuta daga matsalar rashin tsaro.
Haka kuma, an sha yin kira ga hukumomi da su ɗauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Kara karanta wannan
Kano: Fashewar tukunyar gas ta jawo asarar rai, ƴan sanda sun ɗauki matakin gaggawa
Ƴan bindiga sun kafa sansanoni a Katsina
A baya an kawo rahoto mai cewa ƴan bindiga sun kafa sababbin sansanoni a ƙananan hukumomin Bakori da Faskari na jihar Katsina.
Mutanen yankin sun shiga firgici bayan ƴan bindigan sun kori mutanen aƙalla ƙauyuka 10 daga gidajensu sakamakon hare-haren da suke kai wa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng