Rikicin Maida Mai Martaba Sarki kan Sarauta Ya Zo Karshe, Kotun Koli Za Ta Yi Hukunci
- Kotun kolin Najeriya ta zaɓi ranar 6 ga watan Yuni, 2025 domin yanke hukunci kan rikicin sarautar Gwandu da ke jihar Kebbi
- Gwamnatin Kebbi ta nemi kotun ƙoli ta soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wadda ta ba da umarnin mayar da sarkin Gwandu da aka tsige
- Al-Mustapha Jokolo ya na ganin zai iya komawa gadon mulki musamman bayan alkalai sun kuskurantar da tsige shi da aka yi
- Sai dai lauyan basaraken ya roki kotun ta yi fatali da buƙatar gwamnati domin ba ta da kwararan hujjojin da za su sa a soke hukuncin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi - Bayan tsawon shekaru ana fafata shari'a kan batun mayar da Al-Mustapha Jokolo kan sarautar Sarkin Gwandu bayan tsige shi, kotun koli ta shirya warware lamarin.
Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya ranar 6 ga watan Yuni, 2025 domin yanke hukunci kan rikicin sarautar Gwandu, wanda aka shigar gabanta.

Asali: Twitter
Kwamitin alkalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Abba-Aji ce ta sanar da matsayar da suka cimma wa a ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta bayyana cewa dukkan ƙorafe-ƙorafen da aka shigar gabanta kan sarautar Gwandu, za su dogara ne da hukuncin da za ta yanke kan usulin ƙarar.
Ƙarar da gwamnatin Kebbi ta shigar
Tun farko, lauyan gwamnatin jihar Kebbi, Yakubu Maikyau (SAN), ya roƙi kotun da ta ba su dama su ƙara gabatar da hujjoji kan buƙatar neman soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.
Ya nemi Kotun Koli ta soke umarnin da aka bayar na mayar da Jokolo bisa hujjar cewa bai gabatar da ingantattun hujjoji da ke tabbatar da ’yancinsa na komawa kan sarautar ba.
Haka nan, Yakubu Maikyau ya jaddada cewa babbar kotun Kebbi da ta yanke hukunci mayar da sarkin tun a ranar 11 ga Disamba, 2014, ba ta da hurumin sauraron ƙarar.
Don haka a cewar lauyan gwamnati, hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ba shi da inganci kuma ya kamata a soke shi, rahoton Channels tv.
Lauyan Al-Mustapha Jokolo ya yi martani
A nasa ɓangaren, lauya Sylvester Imhanobe Esq, wanda ke wakiltar Al-Mustapha Jokolo, ya roƙi kotun da ta yi fatali da buƙatar da Gwamnatin Kebbi ta shigar.
Ya ce gwamnan Kebbi da kwamishinan shari’a na jihar sun gaza gabatar da hujjojin da za su nuna cewa hukuncin da kotunan baya suka yanke ba daidai ba ne.
A cewarsa, kotunan biyu da suka gabata sun tabbatar da cewa an tsige Al-Mustapha Jokolo ba tare da bin doka ba.
Ya yi nuni da cewa, dokar masarautu (naɗi da tsigewa) ta Kebbi ta tanadi cewa kafin a tube sarki, dole ne a gudanar da cikakken bincike, wanda gwamnati ta gaza yi kafin tsige Jokolo.

Asali: Facebook
A 2005, Babbar Kotun Kebbi ta bada umarni a mayar da Jokolo. Daga bisani kuma, Kotun ɗaukaka ƙara da ke zama a jihar Sokoto a ranar 14 ga Afrilu, 2016 ta tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan
Majalisa ta ayyana kujerun sanatoci 2 a matsayin babu kowa a kansu, ta buƙaci INEC ta canza zaɓe
Ta kuma umarci Gwamnatin Kebbi da ta biya Al-Mustapha Jokolo dukkan hakkokinsa na shekaru 10 da aka cire shi daga sarauta.
Ana jiran ranar 6 ga Yuni, 2025, domin yanke hukunci na ƙarshe kan wannan shari’a a kotun koli.
Rikicin sarauta ya ɓarke a Adamawa
A wani labarin, kun ji cewa an kai gwamnan jihar Adamawa ƙara gaban kotu kan kirkirar masarautar Fufore.
Wasu mutum uku masu mukaman sarauta a masarautar Adamawa ne suka maka Gwamna Ahmadu Fintiri a gaban babbar korun Adamawa, su na kalubalantar kafa masarautar Fufure.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng