Tashin Hankali: Mayakan Lakurawa Sun Kashe Mutane 13, Sun Kona Ƙauyuka 7 a Arewa

Tashin Hankali: Mayakan Lakurawa Sun Kashe Mutane 13, Sun Kona Ƙauyuka 7 a Arewa

  • Yan ta’addan Lakurawa sun farmaki Birnin Dede da ke Kebbi, inda suka kashe mutum 13, sannan suka kona kauyuka bakwai
  • An rahoto cewa maharan sun kai hari kan kauyuka takwas da ke kusa da Birnin Dede, amma sun gaza farmakar ɗaya daga cikinsu
  • Haka kuma, ana zargin zargin harin ya biyo bayan kisan Maigemu, shugaban ‘yan ta’addan Lakurawa, wanda dakarun tsaro suka hallaka
  • Gwamna Nasir Idris ne ya ba dakarun tsaro tallafin da ya taimaka aka kashe Maigemu a yankin Kuncin Baba da ke Arewa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - Al'ummar yankin Birnin Dede da ke jihar Kebbi sun shiga tashin hankali a lokacin da 'yan ta'addar Lakurawa suka kai masu kazamin harin ramuwar gayya.

A ranar Lahadi, 9 ga watan Maris din nan ne aka ce 'yan ta''addan dauke da mugayen makamai suka farmaki kauyen Birnin Dede, inda suka kashe mutane 13.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa cikin gida a Kano, sun yi ta'asa bayan cirewa wani ƴan yatsu

Majiyoyi sun shaida cewa 'yan ta'addar Lakurawa sun kai farmaki jihar Kabbi
Kebbi: 'Yan ta'addar Lakurawa sun hallaka bayin Allah tare da kona gidaje 7. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

'Yan ta'addan Lakurawa sun farmaki Kebbi

Wani mazaunin yankin, Malam Umar ya shaidawa manema labarai cewa maharan sun kuma kai farmaki kauyukan da ke kusa da Birnin Dede, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kauyen Birnin Dede na cikin karamar hukumar Arewa da ke jihar Kebbi.

A cewar Malam Umar, miyagun ‘yan ta’addan sun ƙona akalla kauyuka takwas, amma sun bar ɗaya kacal da ke ƙarƙashin kulawar sojoji.

Mazaunin yankin ya yi ikirarin cewa harin 'yan bindigar na ramuwar gayya ne, bayan kashe shugabansu, Maigemu, da jami’an tsaro suka yi a jihar.

“'Yan ta'adda sun ƙone kauyuka da dama, amma sun bar ɗaya da ke karkashin kulawar sojoji. Allah ne kadai zai kare mu,” inji Malam Umar.

Ana zargin Lakurawa da kai harin ramuwar gayya

Harin na zuwa ne bayan wani farmakin hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro da gwamnatin Kebbi, wanda ya yi sanadin mutuwar shugaban 'yan ta'addar Lakurawa, Maigemu.

Kara karanta wannan

Bayan alkawarin gwamna kan miyagu, jami'an tsaro sun hallaka jagoran Lakurawa

Gwamna Nasir Idris ne ya ba dakarun tsaron duk wani tallafi da suke bukata har ta kai ga an yi nasarar kashe Maigemu a wani yunkuri na dakile ayyukan ‘yan bindiga a Kebbi.

Mun rahoto cewa jami'an tsaro sun kashe hatsabibin dan ta'adda, Maigemu a ranar Alhamis, 6 ga watan Maris, 2025

Majiyoyin leken asiri sun tabbatarwa manema labarai cewa an kashe Maigemu a yankin Kuncin Baba da ke karamar hukumar Arewa, bayan fafatawa mai zafi.

Shugaban karamar hukumar Arewa ya yi magana

Gwamna Nasir na jihar Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris na ba jami'an tsaro gudunmawa wajen kakkabe 'yan ta'adda. Hoto: @NasiridrisKG
Asali: Twitter

Bayan wannan farmakin ne ake zargin ‘yan ta’adda sun mayar da martani ta hanyar kai harin ramuwar gayya kan al’ummar yankin Birnin Dede.

Shugaban ƙaramar hukumar Arewa, Sani Aliyu, ya tabbatar da faruwar harin ga gidan talabijin na Channels TV.

Sai dai kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ya ci tura, domin kakakinta, SP Nafiu Abubakar, bai amsa kiran waya ba.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

Shigowar Lakurawa Najeriya

Yayin da 'yan Arewa ke ci gaba da dandana mummunan sakamakon rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabas da kuma 'yan dadi bindiga a Arewa ta Yamma, an samu bullar 'yan ta'addan Lakurawa a Arewa ta Yamma.

An fara ganin asirin barnar 'yan Lakurawa a shekarar 2024, inda bidiyo da hotuna a kafafen sada zumunta suka yadu da ke nuna ayyukansu na barna.

Masu ruwa da tsaki a bangaren tsaron Najeriya sun sha daukar alkawarin shawo kan matsalolin tsaro, sai dai har yanzu lamarin karuwa yake.

Ana kira ga sulhu da tsageru

A gefe guda, akwai 'yan Najeriya da ke ganin ba da kofar tattaunawa da 'yan ta'adda ka iya kawo karshen barnarsu a dukkan bangarorin kasar.

Cikin wadannan malamai akwai Sheikh Ahmad Gumi, wani fitaccen malamin addini da ke kan gaba wajen tattaunawa da tsageru a Arewa ta Yamma.

Sai dai, gwamnati na kara daura damara wajen kai farmaki maboyar 'yan ta'adda don tabbatar da kakkabe su a kasar.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun kai hari Borno, sun yi barna kafin isowar sojoji

Lakurawa sun kashe 'yan sanda a Kebbi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’addan Lakurawa ne sun kashe ‘yan sanda biyu a jihar Kebbi.

Maharan sun kuma sace shanu fiye da 200 a kauyen Natsini, da ke karamar hukumar Argungu a jihar Kebbi.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan sandan na bakin wani shingen bincike a kan titin Augie/Kangiwa ne lokacin da aka kai harin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin ta hanyar ba da tushen tarihin tsagerun Lakurawa da kuma mafita ga fannin tsaro a babin shawara daga malamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.