Dalilai Masu Karfi Sun Kai Ga Gwamnatin Tinubu Ta Karbe Ragamar Asibitin Kwararru a Gombe

Dalilai Masu Karfi Sun Kai Ga Gwamnatin Tinubu Ta Karbe Ragamar Asibitin Kwararru a Gombe

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana karbe ragamar asibitin kwararru da ke Kuma a jihar Gombe don inganta tasirinsa
  • Gwamnatin ta bayyana dalilai masu karfi da suka kai ga karbe asibitin mai dogon tarihi a karamar hukumar Akko
  • A halin yanzu, jihar Gombe na da asibitocin tarayya guda biyu kenan tun daga karbe tafiyar da na garin Kumo

Jihar Gombe - Gwamnatin Tarayya ta mayar da Asibitin Jaararru nar na garin Kumo, mallakin Gwamnatin Jihar Gombe, zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya.

Wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnatin tarayya na inganta fannin kiwon lafiya a yankin Arewa maso Gabas, wanda ke fuskantar matsaloli da dama a fannin kiwon lafiya.

Sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya ta Kumo ita ce cibiyar kiwon lafiya ta tarayya ta biyu a jihar, bayan Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe, babban birnin jihar.

Tinubu ya karbe ragamar asibitin Gombe a garin Kumo
An karbe ragamar asibitin Kuma a Gombe, ya zama na tarayya | Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Dalilin karbe ragamar asibitin

Wannan ya nuna yadda ake kara daukar matakai don samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar jihar da makwabtansu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan alkawarin gwamna kan miyagu, jami'an tsaro sun hallaka jagoran Lakurawa

Bayo Onanuga, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara na Musamma, wanda ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, ya bayyana cewa asibitin koyarwar tun da farko cibiyar kiwon lafiya ce kafin daga darajarta zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya.

Hakan ya nuna cewa ana iya habaka cibiyoyin kiwon lafiya idan ana da isassun kayan aiki da kuma kulawar da ta dace daga hukumomin kiwon lafiya.

A cewarsa:

"Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya ta Kumo za ta zama babbar asibitin kiwon lafiya, za ta taimaka wajen horas da ma’aikatan lafiya, tare da inganta ayyukan kiwon lafiya a Jihar Gombe da yankin Arewa maso Gabas gaba daya.
"Wannan zai taimaka wajen rage cunkoson marasa lafiya a manyan asibitoci, tare da ba wa al’umma damar samun kulawa cikin sauki."

Yadda aka samar da asibitin

Rahoto ya bayyana cewa, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ne ya nemi a karbi asibitin a karkashin kulawar gwamnatin tarayya.

An kuma ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da bukatar, duba da matsalar mace-macen mata masu juna biyu da jarirai a yankin Arewa maso Gabas da kuma wasu alkaluman kiwon lafiya a Jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ƙara shiga tsaka mai wuya, Majalisar Dokoki ta dawo da shirin tsige shi

An karbe ragamar asibitin Kumo
An karbe ragamar asibitin Kuma a Gombe, ya zama na tarayya | Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Wannan mataki zai taimaka wajen rage mace-macen da ake fuskanta, musamman a yankunan karkara da ke da karancin wuraren kiwon lafiya.

Gwamnatin Tinubu ta yabawa gwamna Inuwa

Gwamnatin Tarayya ta kuma yi la’akari da kokarin da Gwamnatin Jihar ke yi na inganta harkar kiwon lafiya, wanda ya yi daidai da Ajandar Sabunta Fata, wacce ta kunshi gyare-gyare masu zurfi a bangaren kiwon lafiya.

A cikin wannan shiri, ana fatan kara inganta kayan aiki, karin kwararrun likitoci da sauran ma’aikatan jinya domin samar da ingantacciyar kulawa ga marasa lafiya.

Shugaba Tinubu ya yaba wa Gwamna Yahaya bisa fifita jin dadin al’ummar jiharsa, tare da jaddada cewa karbar cibiyar zai inganta tsarin kiwon lafiya a jihar.

Sakamakon da ake fatan sauyin ya haifar

Yayin da wannan mataki ke da nufin inganta kiwon lafiya, ana kuma sa ran bunkasa fannin ilimin likitanci ta hanyar bai wa dalibai dama su koyi ayyukan kiwon lafiya a cibiyar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya daina ɓoye ɓoye, ya jero mutanen da ke jefa matasa harkar ƴan bindiga

Sabuwar cibiyar za ta kuma ba da damar gudanar da bincike kan cututtuka daban-daban da ke addabar yankin Arewa maso Gabas.

Tare da hadin gwiwar hukumomi, an shirya samar da kayayyakin aikin zamani domin tabbatar da cewa ana ba marasa lafiya kulawa daidai da ka'idojin kiwon lafiya na duniya.

An kama ma'aikatan asibiti a Gombe da laifin sata

A wani labarin kuma, kun ji yadda aka kama wasu ma'aikatan asibiti a jihar Gombe bisa zarginsu da aikata sata.

An ruwaito cewa, ana zargin ma'aikatan ne da sace gidan sauro da aka bayar don rabawa talakawa a jihar.

Ba sabon abu bane ganin yadda ma'aikatan asibiti ke sace kayan aiki a asibitoci, ciki har da kayan magani da kayan aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng