Dan gani-kashenin gwamnan Gombe ya fado daga mota a tawaga, ya sheka lahira

Dan gani-kashenin gwamnan Gombe ya fado daga mota a tawaga, ya sheka lahira

  • Wani Ahmed Sagir, dan gani-kashenin gwaman jihar Gombe, Muhammadu Inuwa wanda aka fi sani da Khalifah ya fadi ya mutu a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba
  • Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, tawagar motocin gwamnan suna tafe Khalifah ya fado daga wata mota ta na tsaka da tafiya don zuwa aikin jihar a Bajoga/Funakaye
  • Ya rasa ran sa ne sakamakon karayar da kokon kan sa ya yi, kuma take a nan gwamnan ya umarci motar asibiti ta gaggawa ta wuce da shi asibitin jihar Gombe don duba lafiyarsa

Gombe - Wani Ahmad Sagir wanda aka fi sani da Khalifah mai shekaru 30 wanda dan gani-kashenin gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa ne ya fadi ya rasu a ranar Lahadi, 19 ga watan Satumba.

Ya fado ne daga daya daga cikin motocin tawagar gwamnan suna hanyar zuwa karamar hukumar Bajoga/Funakaye don yin wani aiki, Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An yi ram da wasu ma'aikatan asibiti a Gombe da laifin sace gidan sauron talakawa

Dan gani-kashenin gwamnan Gombe ya fado daga mota a tawaga, ya sheka lahira
Dan gani-kashenin gwamnan Gombe ya fado daga mota a tawaga, ya sheka lahira. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya rasu ne take-yanke bayan kokon kan sa ya fashe. Ba tare da bata lokaci ba gwamnan ya sa motar asibiti ta yi gaggawar wucewa da shi asibitin koyarwa na jihar Gombe don a duba lafiyar sa. Daga nan ne likitoci su ka tabbatar ya rasu bayan isar su asibiti.

A wata takarda wacce darekta janar na harkokin labaran gidan gwamnatin jihar ya saki, Ismaila Una Misilli, ya ce gwamnan ya kwatanta matashin a matsayin “mutum mai girmama jama’a, mai yin aiki tukuru da kuma amana wanda kowa ya san shi a dan gani kashenin APC da ayyukan gwamna Yahaya.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An samu bayanai a kan yadda gwamnan ya dakatar da duk ayyukan ranar don nuna girmamawa ga mamacin wanda aka birne shi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, shafin Linda Ikeji ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin 'yan bindiga a NDA

'Yan bindiga sun sheke rayuka 5, sun raunata wasu 5 a Kebbi

A wani labari na daban, miyagun 'yan bindiga sun halaka rayuka biyar tare da barin wasu biyar da miyagun raunika a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi, Daily Trust ta tattaro.

'Yan bindigan sun tsinkayi kauyen Uchukku a sa'o'in farko na ranar Juma'a, sun sace shanu tare da harbe mutum 5 har lahira.

Wani mazaunin Shanga mai suna Yushau Garba Shanga, ya sanar da Daily Trust cewa, 'yan bindigan sun kai farmaki wurin karfe 1:50 na dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel